‘Wahala Za Ta Kare’, Minista Ya Fadi Yadda Tinubu Ke Kokarin Dakile Halin Kunci

‘Wahala Za Ta Kare’, Minista Ya Fadi Yadda Tinubu Ke Kokarin Dakile Halin Kunci

  • Yayin da al'umma ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, Ministan Bola Tinubu ya fadi yadda shugaban ke korari
  • Karamin Ministan muhalli a Najeriya, Iziaq Kunle Salako ya ce Tinubu ya himmatu wurin kawo karshen halin kunci
  • Ministan ya ce yana da tabbacin irin kokarin da Tinubu ke yi ya dauko hanyar dakile mawuyacin halin da yan kasa ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Karamin Ministan muhalli, Iziaq Kunle Salako ya yi magana kan halin kunci da ake ciki.

Ministan ya ce Shugaba Bola Tinubu ya zaku domin tabbatar da cewa ya yi nasara wurin dakile halin matsin da ake ciki.

Yadda Tinubu ke kokarin shawo kan halin kunci da ake ciki
Bola Tinubu ya tsara hanyoyin kawo karshen mawuyacin hali da ake ciki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Halin kunci: Tinubu ya shirya kawo sauki

Kara karanta wannan

Sanusi II ya magantu kan rigimar matatar Dangote da NNPCL, ya gano masu laifi

Salako ya tabbatar da haka ne a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce kokarin Tinubu wurin inganta wutar lantarki da fadada hanyoyin samun kudi na daga cikin tsare-tsarensa.

Har ila yau, Ministan ya ce Tinubu ya san duk halin da al'ummar Najeriya ke ciki na mawuyacin hali.

Ya ba da tabbacin cewa Shugaba Tinubu zai kawo karshen halin matsin da ake ciki tare da goyon bayan al'ummar kasar.

Minista ya fadi kokarin Tinubu a Najeriya

"Tinubu ya himmatu wurin inganta wutar lantarki da samar da ayyukan raya kasa da kuma fadada hanyoyin samun kudi."
"Hakan zai kara samar da kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa wanda zai tabbatar da inganta tattalin arzikin kasa da rage halin kunci da ake ciki."

Kara karanta wannan

"Ba laifinsa ba ne”: Yakubu Dogara ya yi maganar Tinubu da cire tallafin fetur

- Iziaq Kunle Salako

'Na san halin da ku ke ciki' - Tinubu

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya sani ana cikin wani hali a Najeriya inda ya zargi gwamnatocin baya.

Tinubu ya ce dukan wannan hali da aka shiga na da nasaba da matakan da aka dauka a baya na gwamnatocin Najeriya.

Shugaban ya bukaci hadin kai daga masu ruwa da tsaki da sauran al'ummar Najeriya domin ciyar da kasar gaba da inganta rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.