Hamster Kombat: Alamun da ke Nuna ko Za a Samu Alheri a Mining Inji Masanin Crypto

Hamster Kombat: Alamun da ke Nuna ko Za a Samu Alheri a Mining Inji Masanin Crypto

  • Wani kwararren crypto ya yi tsokaci kan Hamster Kombat da aka haka ba tare da an samu yadda ake so ba
  • Tun kafin a je ko ina, Hussaini Sani Makole ya ce wadanda suka san sha’anin sun san Hamster ba za ta yi daraja ba
  • Malam Hussaini Sani Makole yake cewa tun da aka kirkiro Hamster Kombat babu wasu manyan da suka daura a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Mutanen da su ka yi kokarin hakar Hamster Kombat domin samun sulallar yanar gizo sun gamu da takaici a cikin makon nan.

Mutanen da su ka yi burin samun makudan daloli daga Hamster Kombat kamar yadda aka yi a Notcoin sun ji babu dadi bayan watanni.

Kara karanta wannan

"Wa ka taba ginawa": Tsohon gwamna ga yaronsa gwamnan PDP, ya bugi kirji

Hamster
Hamster Kombat bai yi daraja da ta fashe ba Hoto: www.cryptotimes.io
Asali: UGC

Hamster Kombat: Mun san za a rina Inji masani

Hussaini Sani Makole masani ne a kan sha’anin Crypto, ya yi hira da Daily Nigerian Hausa game da abin da ya faru da Hamster Kombat.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayanisa, Hussaini Makole ya ce alamu tuni sun nuna cewa babu abin kirki da za a samu wajen Hamster Kombat yadda aka ci buri.

Kamar yadda ya ce, za a fahimci haka ne daga adadin sulallan da ware a haka wanda yake cewa sun kai biliyan 100 wanda sun yi yawa.

mutane sun yi wa Hamster Kombat yawa

Bayan yawan da sulallan suka yi wanda yake nuna rashin darajar da ke tafe, ya ce babu wasu manya da suka shiga Hamster Kombat.

Ana gane kimar da sulallen crypto zai yi ne daga irin manyan mutanen da ke tallata shi.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya magantu kan rigimar matatar Dangote da NNPCL, ya gano masu laifi

Wani dalili da ya kawo kuma shi ne babu wata mafita da Hamster Kombat ta kawo a duniyar Crypto, wannan ya kara haska masu lamarin.

Crypto sa'a ko damfara?

Abubakar Fogu ya yi magana a Facebook, yake cewa dama harkar Crypto ba komai ba ce face zamba, ana yaudarar mutane a yanar gizo.

“Crypto ba komai bane sai zamba cikin hikima cikin mining 100 da kyar kasamu guda uku nagartatu masu gaskiya.
"Ko Shi notcoin anyi shi domin yaudara mutune so amince da mining yana bada kudi kuma karyane, zamba ne da yaudara. Tun da ka fara Ban da notcoin wani project ne mai gaskiya?”

- Abubakar Fogu

Shin Hamster Kombat tayi daraja?

Abdulrahman Baba Ahmad a shafin Facebook ya ce Hamster Kombat ba rashin kima ta yi ba, sai dai kurum mutane sun yi masu yawa ne.

Malam Abdulrahman Baba Ahmad ya na ganin Hamster Kombat zai yi nasara a duniyar wasannin Crypto da yanzu su ke tashe a duniya.

Kara karanta wannan

Dalilan da suka jawo fetur yake tsada duk da samuwar matatar Dangote Inji Injiniya

An cafke wani 'dan crypto

Kwanakin baya aka ji labari rundunar 'yan sanda ta dura kan shahararren dan crypto a Najeriya, 'yan sanda suna zarginsa da laifi.

An yi ram da Linus William da aka fi sani da Blord wanda ya yi suna a shafukan sada zumunta da zargin daukar nauyin ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng