Zanga Zangar Oktoba: Matasan Arewa Sun Fadi Matsayarsu kan Hawa Tituna

Zanga Zangar Oktoba: Matasan Arewa Sun Fadi Matsayarsu kan Hawa Tituna

  • Kungiyar matasa a Arewa ta janye daga shiga zanga-zangar da ake shirin yi a ranar Talata 1 ga watan Oktoban 2024
  • Kungiyar Arewa Youths for Peaceful Coexistence ta shawarci masu shirin yin zanga-zangar da su nemo hanyar tattaunawa
  • Wannan na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tarayya ke neman hanyoyin shawo kan matasan game da shirin zanga-zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar matasa a Arewa sun bayyana matsayarsu kan fita zanga-zanga a mako mai zuwa.

Kungiyar matasan da ake kira Arewa Youths for Peaceful Coexistence (AYPC) ta yi fatali da zanga-zangar da za a yi.

Matasan Arewa sun magantu kan shirin zanga zangar Oktoba da za a yi
Wata kungiyar matasan Arewa ta janye daga shiga zanga-zanga. Hoto: Nurphoto.
Asali: Getty Images

Zanga-zanga: Matasa sun shirya hawa tituna

Punch ta ruwaito cewa matasa na shirin sake yin zanga-zangar a ranar Talata 1 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga matsala ana shirin zanga-zanga, Gwamnatin Tinubu ta yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin kunci da ake ciki ne ya tilasta mutane yin zanga-zangar a ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

Shugaban kungiyar AYPC reshen Abuja, Ogah Mark Okpanachi shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.

Okpanachi ya shawarci masu shirin zanga-zangar da su nemo hanyar tattaunawa madadin fita tituna da ta da tarzoma, cewar rahoton Tribune.

Matasan Arewa sun janye daga shiga zanga-zanga

"Mu na tare da ku a ko da yaushe, mu na magane ne a matsayinmu na yan Najeriya da ke fatan zaman lafiya a Najeriya."
"Mu ne Arewa Youth for Peaceful Coexistence mun zo nan ne domin jawabi kan shirin zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoba."
"Ina kira ga matasa da su sake duba kan shirin zanga-zanga wanda zai iya jawo rigima da rashin zaman lafiya a cikin kasa."

Kara karanta wannan

'Babu ja da baya', Dan takarar shugaban kasa ya sha alwashin fita zanga zanga

- Ogah Mark Okpanachi

Sowore ya shirya jagorantar zanga-zanga

Kun ji cewa ana shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Omoyele Sowore ya sha alwashin jagorantar al'umma hawa tituna.

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce dole su fita zanga-zangar saboda halin kunci da shugabannin suka jefa al'umma a ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin sake fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 saboda halin kunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.