‘Sarkin ne Mai Daraja Ta 1’, Ganduje Ya Kwatanta Masarautar Bichi da Ta Sanusi II

‘Sarkin ne Mai Daraja Ta 1’, Ganduje Ya Kwatanta Masarautar Bichi da Ta Sanusi II

  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kai ziyarar jaje masarautar Bichi da ke jihar Kano a yau Asabar
  • Ganduje ya jajantawa iyalan jami'an yan sanda da suka mutu yayin dawowa daga zaben jihar Edo da aka gudanar
  • Tsohon gwamnan Kano ya bayyana yadda ya ke kallon masarautar Bichi inda ya ce sarki mai daraja ta daya ne ke jagorancinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan masarautar Bichi da ke jihar.

Shugaban APC ya bayyana cewa a wurinsa a masarautar Bichi, sarki ne mai daraja ta daya yake jagorantarta.

Ganduje ya ba da gudunmawa ga iyalan yan sanda a Bichi da ke Kano
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan yan sanda a Bichi da ke jihar Kano. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Ganduje ya jajanta da mutuwar yan sanda

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon yadda daruruwan mutane suka tarbi Ganduje a Kano

Ganduje ya bayyana haka yayin ziyarar jaje a karamar hukumar bayan mutuwar wasu jami'an yan sanda, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Kano ya nuna damuwa kan mutuwar yan sanda inda ya ce tabbas an yi babban rashi.

Daga bisani ya ba da gudunmawar N20m ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin.

"Mun zo nan ne ba domin murna ba sai dai jaje ga sifetan yan sanda da jihar Kano da kuma iyalan wadanda suka mutu."
"Na yanke shawarar zuwa na musamman saboda girman mutuwar kuma sun mutu ne yayin da suke aikin bautar kasa."
"A wuri na, masarautar Bichi tana da sarki mai daraja ta daya ne."

- Abdullahi Ganduje

Musabbabin ziyarar Ganduje jihar Kano

Hakan ya biyo bayan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar jami'an yan sanda akalla guda biyar daga jihar Kano.

Rahotanni sun ruwaito cewa yan sandan sun rasa rayukansu ne yayin da suke dawowa daga jihar Edo bayan kammala zabe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami’an gidan yari 4, ta fadi dalili

Jami'an yan sandan kamar yadda hukumar FRSC ta tabbatar sun gamu da hatsarin a hanyar Zaria zuwa Kano.

Daruruwan mutane sun tarbi Ganduje a Kano

A wani labarin, Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kai ziyara jihar Kano domin jaje bayan hatsarin da jami'an yan sanda suka yi.

Daruruwan al'umma ne suka tarbi tsohon gwamnan jihar a karamar hukumar Bichi a yau Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.