Borno: Wani Kwamandan Boko Haram Ya Mika Wuya Ga Sojoji

Borno: Wani Kwamandan Boko Haram Ya Mika Wuya Ga Sojoji

  • Wani gawurtaccen ɗan ta'addan Boko Haram, Bochu Abacha ya ajiye makamai, ya miƙa wuya ga rundunar sojojin haɗin guiwa a Borno
  • A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rundunar MNJTF ya ce Bochu ya jima yana addabar mutane a titin Mongunu-abaga
  • Ya ce tubabben ɗan ta'addan ya fara bai wa sojoji haɗin kai da bayanan sirri, an kwato makamai da kudi daga hannunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Wani ƙasurgumin ɗan ta'adda kuma kwamanda a Boko Haram, Bochu Abacha ya miƙa wuya ga rundunar sojojin haɗin guiwa MNJTF.

Wannan ba ƙaramar nasara bace a yakin da dakarun sojojin ke yi da ƴan ta'adda a yankin tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Arewa na cikin matsala, ambaliya ta ƙara kashe mutum 29, gidaje 321,000 sun lalace

Dakarun sojoji.
Wani hatsabibin ɗan Boko Haram ya mika wuya ga sojoji a Borno Hoto: Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce kwamandan Boko Haram ya mika wuya ne ga rundunar haɗin guiwar da aka tura wanzar da zaman lafiya a ƙaramar hukumar Kukawa ta Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun MNJTF, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, 28 ga watan Satumba, 2024.

Yadda ɗan ta'addan ya miƙa wuya a Borno

Osoba ya ce ɗan ta'addan ya shahara daga cikin mayaƙan Boko Haram, wanda ke yawan jagorantar kai hare-haren ta'addanci a titin Mongunu-Baga.

"Bochu Abacha ya kasance ƙasurgumin ɗan ta'adda wanda yana ɗaya daga cikin ƴan Boko Haram da ke kai hare-hare a tsakanin Mongunu zuwa Baga.
"Ya yi bayanin cewa ya miƙa wuya ne sakamkon matsin lambar dakarun MNJTF da kuma tubar da ya yi, inda ya ce ya gudo daga sansanin Boko Haram na Mussaram tare da bindigarsa."

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu, ta tabbatar da naɗin CJN a Najeriya

Sojoji sun kwato makamai a hannunsa

Abubuwan da aka kwato daga Bochu sun hada da bindiga kirar AK 47, Magazine cike da harsashi, wayar hannu, layin AIRTEL da kuma kudi N32,500.

Yanzu haka yana bai wa dakarun sojojin bayanan sirri game da ayyukan ƴan ta'adda a yankin, rahoton Daily Post.

Jami'an tsaro sun ceto manoma a Katsina

A wani rahoton kuma jami'an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da wasu manoma da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Katsina.

Manoman guda shida da suka haɗa da mata uku da yara uku an yi garkuwa da su ne a kusa da ƙauyen Gurbin Magarya da ke ƙaramar hukumar Jibia ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262