Hotuna da Bidiyon Yadda Daruruwan Mutane Suka Tarbi Ganduje a Kano

Hotuna da Bidiyon Yadda Daruruwan Mutane Suka Tarbi Ganduje a Kano

  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kai ziyara jihar Kano domin jaje bayan hatsarin da jami'an yan sanda suka yi
  • Daruruwan al'umma ne suka tarbi tsohon gwamnan jihar a karamar hukumar Bichi a yau Asabar 28 ga watan Satumbar 2024
  • Wannan na zuwa ne bayan jami'an yan sanda sun gamu da hatsarin mota yayin dawowa daga zaben jihar Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Daruruwan mutane ne suka fito a jihar Kano domin tarbar shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje ya kai ziyara karamar hukumar Bichi da ke jihar a yau Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya kai ziyara jihar Kano
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi ya samu tarba ta musamman a jihar Kano. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Ganduje ya kai ziyara a Kano

Kara karanta wannan

'Sarkin ne mai daraja ta 1', Ganduje ya kwatanta masarautar Bichi da ta Sanusi II

Daily Trust ta wallafa hotunan yadda aka tarbi Ganduje yayin ziyarar jaje game da hatsarin jami'an yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu jami'an yan sanda sun yi hatsari yayin dawowa daga zaben jihar Edo.

Hakan ya biyo bayan gudanar da zaben jihar a ranar Asabar 21 ga watan Satumbar 2024 da jam'iyyar APC ta yi nasara.

Hukumar FRSC ta yi magana kan hatsarin

Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) ita ta tabbatar da mutuwar yan sanda a ranar Talata 24 ga watan Satumbar 2024.

Hukumar ta ce hatsarin ya rusa da jami'anta guda biyar yayin da suke dawowa daga jihar Edo bayan kammala zaben gwamna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a kauyen karfi da ke kan hanyar Zaria zuwa Kano kusa da filin fakin na tireloli.

Kara karanta wannan

Abba ya yiwa Ganduje illa a siyasa, tulin 'yan APC sun sauya sheka a mahaifarsa

Hotunan yadda aka tarbi Ganduje a Kano:

Ganduje
Ganduje
Ganduje
Ganduje
Ganduje

Ganduje ya jagoranci gwamnonin APC zuwa Abuja

Kun ji cewa bayan kammala zaben Edo, shugaban APC, Abdullahi Ganduje zai gabatar da zaɓaɓɓen gwamna, Monday Okpebholo ga Shugaba Bola Tinubu.

Ganduje ya jagoranci gwamnonin APC zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024 bayan kammala zaben jihar.

Daga cikin wadanda suke cikin tawagar sun hada da Sanata Adams Oshiomhole da ke wakiltar Edo ta Arewa da mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.