Kano: Sarki Sanusi II Zai Yi Wa ‘Ya ‘Yan Ado Bayero da Wasu Hakimai Sauyin Sarauta

Kano: Sarki Sanusi II Zai Yi Wa ‘Ya ‘Yan Ado Bayero da Wasu Hakimai Sauyin Sarauta

  • An rahoto cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi na’am da wasu nadin sarauta da za a yi a makon gobe
  • Mai martaban zai karawa wasu masu rike da sarauta girma, Falakin kasar Kano ya na cikin wadanda aka zaba
  • Bashir Ado Bayero da Bello Ado Bayero za su zama ‘Dan Isa da ‘Dan Lawan Kano a sauyin da zai shafi mutane 14

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Muhammadu Sanusi II zai yi nade-naden sarauta a jihar Kano, kusan wannan shi ne mafi girma bayan dawowarsa karaga.

Bayanan da aka samu sun nuna an gabatar da canje-canje 14 wadanda mai martaba Muhammadu Sanusi II ya amince da su.

Muhammadu Sanusi II
Sarki Muhammadu Sanusi II zai yin nadin sarauta a Kano Hoto: Ibrahim Sanyi Sanyi
Asali: Facebook

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zai yi nade-nade

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yiwa Jonathan martani kan tsige shi daga gwamnan CBN a 2013

Sa’adatu Baba Ahmed ta fitar da sanarwar a shafinta na Facebook a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda masoyiyar Mai martaban ta bayyana, za a shirya bikin daga sarautar tasu a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoban 2024.

Dan Buran Kano, Munir Sanusi Bayero zai zama Wambai yayin da Galadima, Haruna Rasheed Sanuzi zai koma ‘Dan Iyan Kano.

Abdullahi Lamido Sanusi wanda yake rike da sarautar Turaki zai zama ‘Dan Barden Kano.

Shi kuma Kabiru Tijjani Hashim zai bar sarautar Dan Isan Kano ya zama Turakin Kano, Yahaya Inuwa Abbas zai zama Dan galadima.

Sauran wadanda za a karawa sarauta a Kano

Daga cikin wadanda majalisar Sarkin Kano ta amince a karawa girma akwai Bunun Kano, Dan Buram, Dan Isa da kuma Dan Darma.

Ibrahim Hamza Bayero zai zama ‘Dan Majen Kano, sarautar da Muhammadu Sanusi II ya rike kafin fara zama Sarki a Yunin 2014.

Kara karanta wannan

El Rufai ya fadi yadda ya ji bayan dawo da Sanusi II sarautar Kano da aka tuge a 2020

Abdullahi Abubakar Bayero zai koma Dan Darman Kano daga sarautarsa ta Yariman Kano.

Falakin Kano, Alhaji Mujitaba Abba zai zama Sarkin Yakin Kano sai shi kuma Fagacin Kano zai zama Katuka a nadin da za a yi.

A karshe kuma Ambasada Ahmed Umar wanda shi ne ‘Dan Maliki zai zama Jarman Kano.

Sanarwar nadin sarauta a Kano

"Ana gayyatar al’umma daga kowanne ɓangare na ƙasashen ƙetare da Najeriya da kuma jihar Kano, zuwa wajen shagalin bikin naɗe-naɗen hakimai goma sha huɗu da Mai martaba Sarkin Kano Dr. Khalifa Muhammad Sanusi II, CON, zai ɗaga martabar sarautarsu, a ranar 4/10/2024 da misalin ƙarfe tara na safe a babbar fadar Kano da ke Ƙofar Kudu a jihar Kano.
"Masu girma hakimai Allah ya kama"

- Sa’adatu Baba Ahmad.

Sanusi II a kan matatar Dangote da NNPCL

Rahoto ya zo cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da matatar Aliko Dangote da ake ta samun sabani da kamfanin NNPCL.

Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda ake neman dakile cigaban da matatar za ta kawo, ya ce wasu manya ke kokarin hana ruwa gudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng