Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutum 9 a Sabuwar Hukumar da Aka Kafa a Arewa

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutum 9 a Sabuwar Hukumar da Aka Kafa a Arewa

  • Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ƴan majalisar gudanarwa a hukumar raya Arewa maso Yamma watau NWDC ranar Asabar
  • Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa, ya ce ana sa ran waɗanda aka naɗa za su ba da gudummuwa wajen bunƙasa yankin
  • A watan Yuli, 2024 ne Shugaba Tinubu ya rattaba hannu a kudirin dokar kafa hukumar NWDC bayan majalisa ta amince

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa majalisar gudanarwa ta farko a sabuwar hukumar raya shiyyar Arewa maso Yamma (NWDC)

Shugaban ƙasar ya aika sunayen mutum tara da ya naɗa a hukumar ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da naɗinsu.

Kara karanta wannan

"An samu canji": Hukumar alhazai, NAHCON ta sanar da sabon tsarin aikin hajjin 2025

Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu ya nada majalisar gudanarwa a hukumar raya Arewa maso Yamma Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a shafinsa na manhajar X yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya kafa hukumar NWDC

Sanarwar ta ce wannan naɗe-naɗen na zuwa ne biyo bayan rattaɓa hannun da dhugaban ƙasar ya yi kan kudirin kirkiro hukumar raya Arewa maso Yamma a watan Yuli.

Naɗa majalisar gudanarwa ta sabuwar hukumar wata babbar alama ce da ke nuna nan da ba daɗewa ba za ta fara aiki gadan-gadan.

Jerin waɗanda Tinubu ya naɗa

Tinubu ya zabi Haruna Ginsau (Jigawa) a matsayin shugaban majalisar da Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano) a matsayin Manajan Darakta/Babban jami’in gudanarwa na hukumar.

Sauran ƴan majalisar sun hada da Dr. Yahaya Namahe (Sokoto), Aminu Suleiman (Kebbi), Tijjani Kaura (Zamfara), Abdulkadir Usman (Kaduna), Muhammad Wudil (Kano), Shamsu Sule (Katsina), da Nasidi Ali (Jigawa).

Kara karanta wannan

Shirin zanga zanga a watan Oktoba ya girgiza gwamnatin Tinubu, an fara lallaɓa matasa

Onanuga ya ce:

"Ana fatan waɗanda aka naɗa a majalisar gudanarwar za su yi amfani da gogewarsu wajen bunƙasa yankin Arewa maso Yamma.

Ya yi nuni da cewa hukumar ta NWDC za ta mayar da hankali wajen samar da ci gaba, bunƙasa tattalin arziki, da kyautatawa al’umma a yankin.

Tinubu ya naɗa daraktocin NTA

Kuna da labarin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin manyan daraktoci bakwai a gidan taabijin na Najeriya (NTA).

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya sanar da haka ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262