Jami'an Tsaro Sun Ceto Manoman da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Su a Katsina
- Jami'an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da wasu manoma da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Katsina
- Manoman guda shida da suka haɗa da mata uku da yara uku an yi garkuwa da su ne a kusa da ƙauyen Gurbin Magarya da ke ƙaramar hukumar Jibia ta jihar
- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina a cikin wata sanarwa ya yaba da ƙoƙarin da jami'an tsaron suka yi wajen ceto manoman daga hannun ƴan bindigan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun ceto wasu manoma shida da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Katsina.
Manoman da suka haɗa da mata uku da yara uku ƴan bindiga sun yi garkuwa da su ne lokacin da suke girbin masara a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an sace manoman ne a ranar, 26 ga watan Satumban 2024 a kusa da ƙauyen Gurbin Magarya, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka ceto manoma a hannun ƴan bindiga
Jami'an tsaron da suka ceto su sun haɗa da na rundunar KSWC, sojoji, ƴan sanda, DSS, NSCDC bayan sun bi sahun ƴan bindigan.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr. Nasir Mu'azu ya yaba da ƙoƙarin jami'an tsaron da ƴan banga.
A cikin wata sanarwa, ya yaba da jajircewarsu da ɗaukin da suka kai cikin gaggawa wanda ya tabbatar da cewa manoman sun sake haɗuwa da iyalansu.
Gwamnatin jihar ta kuma sake ba da tabbaci kan jajircewarta wajen tabbatar da kare rayukan jama'a, musamman waɗanda suke zaune a yankunan da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga.
An ƙara tsaurara tsaro
Mataimakin shugaban kwamitin tsaro na ƙaramar hukumar Jibia ya tabbatarwa Legit Hausa ceto manoman daga hannun ƴan bindiga.
Malam Nasiru Jibia ya bayyana cewa jami'an tsaron sun bi sahun ƴan bindigan ne bayan sun ɗauke manoman a gona.
"Eh dama mun ƙara sanya ƴan banga a wuraren gonaki domin jama'a su samu su girbi amfanin da suka shuka. Bayan sun samu labarin sace mutanen sai suka bi sahunsu inda suka samu nasarar ceto su."
- Malam Nasiru Jibia
Jami'an tsaro sun hallaka ɗan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaron Najeriya sun kara yin nasarar hallaka wani jagoran ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin kasar nan.
Gawurtaccen ɗan bindiga mai suna Kachalla Makore ya gamu da ajali ne a lokacin da ya jagoranci zuwa ɗauko gawar wanda ƴan banga suka kashe, Sani Black.
Asali: Legit.ng