Cin Hancin N15m: Majalisar Wakilai ta Gayyaci Shugaban EFCC da Wasu Mutum 2

Cin Hancin N15m: Majalisar Wakilai ta Gayyaci Shugaban EFCC da Wasu Mutum 2

  • Majalisar Wakilai ta soma bincike kan zargin da ake yiwa wasu jami'an EFCC Kwanturola Janar Haliru Nababa na karbar cin hanci
  • Majalisar ta gayyaci shugaban EFCC, Ola Olukoyede, biyo bayan ikirarin da Bobrisky ya yi na cewa wasu jami’ai sun karbi rashawar N15m
  • Bangarorin da abin ya shafa a wannan zargi za su gurfana a gaban majalisar wakilan a ranar Litinin, 30 ga Satumba domin amsa tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta kuduri aniyar gudanar da bincike kan zargin karbar rashawa da ake yiwa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Bayan kudurin, kwamitin hadin gwiwa na majalisar ya mika goron gayyata ga shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode.

Kara karanta wannan

Yemi Cardoso ya yi rugu rugu da darajar Naira cikin watanni 12 a Bankin CBN

Zargin cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta dauki mataki kan jami’an EFCC, Bobrisky da VeryDarkMan
Majalisar wakilai za ta binciki zargin cin hancin N15m tsakanin jami'an EFCC, VDM da Bobrisky. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa ta gayyaci EFCC, NCoS

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 27 ga Satumba 2024, kwamitin ya bukaci shugaban hukumar EFCC ya gurfana gabanta, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, majalisar ta bukaci babban kwanturolan hukumar gidajen gyaran hali ta kasa (NCoS) da ya bayyana gabanta a ranar Litinin 30 ga wata.

An ce majalisar ta bukaci shugabannin hukumomin biyu da su taho tare da dukkanin jami’an da ke da hannu a wannan zargi.

Ana zargin jami'ai da karbar rashawa

Zargin karbar cin hancin da ake yiwa hukumar EFCC da kuma hukumar gidajen yarin ya biyo bayan wata tattaunawa da aka yi da dan daudu, Idris Okuneye (Bobrisky).

Tattaunawar ta nuna cewa Bobrisky ya biya N15m ga EFCC domin ta janye tuhumar da ta ke masa na safarar kudi, kuma bai yi rayuwar gidan yari tare da sauran fursunoni ba.

Kara karanta wannan

Litar fetur ta koma N2500 bayan an fusata 'yan kasuwa, gwamnati ta dauki mataki

Har ila yau, kwamitin majalisar yana gayyatar Bobrisky da wani mai tasiri a shafukan sada zumunta, Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, wanda ya fitar da tattaunawar.

An dakatar da jami'an gidan yari

Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta dakatar da wasu jami'anta bisa zarginsu da karbar cin hanci da rashawa.

An ce hukumar ta dakatar da manyan jami'an hudu bayan Idris Okuneye watau Bobrisky ya zargi hukumar gidajen yarin da karbar masa Naira miliyan 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.