Darajar Naira Ta Yi Raga Raga a Kasuwa, Ta Yi Faduwa Mafi Muni cikin Watanni 7

Darajar Naira Ta Yi Raga Raga a Kasuwa, Ta Yi Faduwa Mafi Muni cikin Watanni 7

  • Naira ba ta ji da daɗi ba a hannun Dalar Amurka a kasuwar ƴan canji a ranar Juma'a, 27 ga watan Satumban 2024
  • Darajar Naira ta koma N1,700/$ wanda wannan ita ce faɗuwa mafi muni da ta yi tun daga watan Fabrairun 2024
  • Sai dai, a farashin gwamnati darajar Naira ta ƙaru da kaso 2.24% daga kan farashin da aka sayar da ita a ranar Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Darajar Naira ta ragu zuwa N1,700 kan kowace Dala a kasuwar ƴan canji a ranar Juma'a.

A ƙarshen sa’o’in ciniki, darajar Naira ta ragu da kaso 1.49% idan aka kwatanta da N1,675/$ da aka yi cinikinta a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yemi Cardoso ya yi rugu rugu da darajar Naira cikin watanni 12 a Bankin CBN

Darajar Naira ta fadi a kasuwa
Darajar Naira ta koma N1,700/$a kasuwar canji
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darajar Naira ta faɗi warwas a kasuwa

Jaridar The Cable ta ce faɗuwar darajar Naira zuwa N1,700 kan kowace Dala ita ce mafi faɗuwar da ta yi tun ranar 19 ga Fabrairu, lokacin da ta koma N1,730/$.

Ƴan canji a kasuwar canji da ke Legas, suna siyan kowace Dala a kan N1,680/$ da kuma sayarwa a kan farashin N1,700/$, inda suke samun ribar N20.

A kasuwar ƴan canji a ranar Litinin, darajar Naira ta ragu zuwa N1,665/$ daga farashin N1,663/$ da aka yi cinikinta a ranar, 20 ga watan Satumba.

Darajar Naira ta ƙara raguwa zuwa N1,670 a ranar Talata sannan ta ƙara raguwa zuwa N1,680 a ranar Laraba.

Sai dai, darajar Naira ta farfaɗo zuwa N1,675 a ranar Alhamis.

Naira ta farfaɗo a farashin gwamnati

A farashin gwamnati, darajar Naira ta ƙaru da kaso 2.24% daga farashin N1,576.1/$ da aka yi cinikinta a ranar Alhamis zuwa kan farashin N1,540.78 a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Masu shirya sabuwar zanga zanga sun aika saƙo ga ƴan sandan Najeriya

A cewar bayanai daga FMDQ, an siyar da Dala kan farashi mafi tsada na N1,691/$ da farashi mai rahusa na N1,530/$ a lokacin sa'o'in ciniki.

Darajar Naira ta faɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa darajar Naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar hada-hadar musayar kudin ƙasashen ketare da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Najeriya.

Bayanai sun nuna cewa darajar kuɗin na Najeriya ta ragu zuwa N1,639.41/1$ a farashin gwamnati a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng