An Yi Kuskure: Buba Galadima Ya Ambaci Dan Takarar Shugaban Kasa Daya da Ya Fi Tinubu Nagarta

An Yi Kuskure: Buba Galadima Ya Ambaci Dan Takarar Shugaban Kasa Daya da Ya Fi Tinubu Nagarta

  • Jigon jam’iyyar adawa ta NNPP, Buba Galadima ya ce idan da abokin siyasarsa, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya zama shugaban kasa a Najeriya da yanzu kowa ya dandana romon dimokradiyya
  • Galadima ya ce, zaman Kwankwaso shugaban kasa zai taimaka wajen yaki da ci baya tare da habaka kasa ta ci gaba tare da ‘ya’yanta
  • Legit ta ruwaito cewa, matsin tattalin arziki ne ke kan gaba a mulkin Tinubu yayin da ya cika shekara guda a shugabancin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja – Buba Galadima, jigon siyasar jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa, da ace Rabiu Kwankwaso ne ya zama shugaban kasa, da zai yi abin da shugaba Bola Tinubu ya gaza yiwa ‘yan Najeriya.

Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba, Galadima ya ce galibin wadanda Tinubu ya ba mukami ba yiwa Najeriya aiki ne a gabansu ba, sai dai burin cika aljihunsu.

Kara karanta wannan

"Aljihunsu kawai suka sani," Buba Galadima ya tona asirin ministoci da hadiman Tinubu

An fadi mutumin da ya fi Tinubu nagarta
Kwankwaso ya fi Tinubu nagarta | Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Babu wanda yake da muradi kan Najeriya sai dai aljihunsa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauyin da ake bukata a Najeriya

Da aka tambaye shi ta yadda za a samu sauyi a Najeriya, Galadima ya ce:

“Tunani ne. Ka nuna misali a matsyainka na shugaba. Ka kula da na kasa; je ka Kano ka ga yadda ake horar da mutane a cibiyar koyar da sana’a ta Dangote. Suna koyawa matasa maza sana’o’i.”

Idan baku manta ba a 2022, Legit ta ruwaito cewa, Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya shiga NNPP da zimman kujerar shugaban kasa.

Kwankwaso ne na hudu a zaben 2023

A nan ne ya yi takara a zaben fidda gwani, kuma aka mika masa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ya gabata tare da abokin takararsa Bishop Isaac Idahosa. Sun yi na hudu a zaben 2023 tare da kuri’u miliyan 1.5.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya magantu kan rigimar matatar Dangote da NNPCL, ya gano masu laifi

Kwankwaso dai ya kasance gwamna a Kano, inda ya yi mulki tsakanin 1999 zuwa 2023 da kuma 2011 zuwa 2015 a karo na biyu.

Daga baya, an zabe shi a kujerar sanata a 2015, inda ya kasance a jam’iyyar APC yana wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Duba bidiyon Buba Galadima a nan:

Niyyar Kwankwaso a zaben 2027

A wani labarin, Kwankwaso ya ce babban abin da ya saka a gaba shi ne ceto Najeriya daga halin matsin tattalin arziki da take ciki.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara ofishin NNPP a jihar Osun, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Jigon jam'iyyar NNPP wanda ya samu wakilcin Dakta Rahila Mukhtar ya ce jam'iyyar ta shirya tsamo yan Najeriya a takaici, cewar rahoton Daily Post.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.