Shirin Zanga Zanga a Watan Oktoba Ya Girgiza Gwamnatin Tinubu, An Fara Lallaɓa Matasa

Shirin Zanga Zanga a Watan Oktoba Ya Girgiza Gwamnatin Tinubu, An Fara Lallaɓa Matasa

  • Gwamnatin tarayya ta fara lallaba masu shirya zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 domin gudun shiga wata sabuwar matsala
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu ƴan Najeriya ke shirin sake fantsama kan tituna domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa
  • A watan Agusta da ya wuce, matasa sun gudanar da irin wannan zanga-zanga daga ranar 1 zuwa 10 ga wata a mafi yawan jihohin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kamar yadda aka saba, Talata, 1 ga Oktoba, 2024 za ta kasance ranar farin ciki, bisa ga al'ada, don murnar samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka a 1960.

Sai dai alamu sun nuna ranar ƴancin kai ta wannan shekarar 2024 da Najeriya ke cika shekaru 64 na iya banbanta da yadda aka saba murna da farin ciki.

Kara karanta wannan

Shirin zanga zangar 1 ga Oktoba ya kankama, an aika sako ga 'yan sanda

Shugaba Tinubu da masu zanga zanga.
Gwamnatin Tinubu ta fara kokarin shawo kan masu shirya zanga zangar 1 ga watan Oktoba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a ɓangare guda, gwamnatin tarayya na shirye-shiryen gudanar da bukukuwan da aka saba domin murnar zagayowar wannan rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa na shirya zanga-zanga a ranar ƴanci

Amma a ɗaya bangaren, wasu ƴan Najeriya sun yi nisa a shirin fita zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, wanda suka ce ya samo asali daga rashin shugabanni na gari.

An gudanar da irin haka a tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta, inda dubban matasa a jihohi da dama suka fantsama kan tituna suka gudanar da zanga-zangar.

Abubuwan da suka damu ƴan Najeriya

Daga cikin abubuwan da masu zanga-zangar suka koka sun kunshi cire tallafin mai, faɗuwar darajar Naira da ƙarin kudin wutar lantarki.

Sai dai duk da zanga-zangar da ake shirin yi ranar Talata na kara matsowa babu wani yunƙuri kamar wanda aka yi a baya, inda malamai, sarakuna da manya suka sa baki.

Kara karanta wannan

Zanga zangar Oktoba: Matasan Arewa sun fadi matsayarsu kan hawa tituna

Fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnati ta fara tattaunawa da wadanda suka shirya zanga-zangar da nufin samun fahimtar juna da su kafin ranar 1 ga watan Oktoba.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ya faɗi haka da yake amsa wasu tambayoyi da aka aika masa.

Zanga-zanga: Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

"Gwamnati ba ta adawa da duk wata zanga-zangar lumana da ‘yan Najeriya za su yi. Baya ga haka ma suna da haƙƙin yin zanga-zanga.
"Amma tana fargabar zanga-zangar ta canza zani ta koma tashin hankali kamar yadda aka gani a watan Agusta, 2020 lokacin zanga-zangar EndSARS.
"Hukumomin tsaro sun fara zama da waɗanda ke shirya zanga zangar kuma ana sa masu ido don gudun kada su jefa ƙasar ciki rudani ko su bari a yi amfani da su wajen ruguza Najeriya."
"Muna tabbatarwa ƴan Najeriya cewa akwai haske a gaba, bayan wuya sai daɗi don haka su ƙara hakuri da fahimta."

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga matsala ana shirin zanga-zanga, Gwamnatin Tinubu ta yi magana

- Bayo Onanuga.

Wani matashi a Katsina, wanda ya shiga zanga-zangar da aka yi a watan Agusta ya ce wannan karon ba zai fita ba.

Matashin mai suna, Kwamared Ahmad Kabir, ɗan kungiyar NYCN ya ce wancan karon ya yi dana sani saboda gaba ɗaya zanga-zangar ta sauka daga manufarta.

Ya ce:

"Eh na ji labarin ana shirin zanga-zanga a Oktoba, ban sani ba ko za a yi a nan Katsina amma dai wannan karon sai dai mu ce a tashi lafiya.
"Manufar zanga-zangar daban abin da ake yi daban shiyasa ko wancan karon ni dai ban ji daɗi ba, Allah ya kawo mana sauƙi, ina fatan a yi lafiya a gama lafiya."

Legas: Ƴan sanda sun gayyaci shugaban matasa

A wani rahoton kuma yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024, yan sanda a Lagos sun gayyaci shugaban matasa.

Kwamishinan yan sanda a jihar, Olanrewaju Ishola ya ce sun dauki matakin ne domin tattauna wasu batutuwa kan lamuran kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262