"N77,000 Ya Yi Kaɗan": An Bayyana Kuɗin da Ya Kamata Gwamnati Ta Biya Mata Ƴan NYSC
- Sanata Shehu Sani ya yi martani kan ƙarin alawus da gwamnatin tarayya ta yi wa matasa ƴan NYSC daga N33,000 zuwa N77,000
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce ƙarin alawin abin a yaba ne amma mata ƴan NYSC sun cancanci fiye da haka
- Shehu Sani ya bayyana dalilin da ya sa yake ganin ya kamata a rika biyan mata masu hidimtawa ƙasa alawus fiye da N77,000 a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta ƙarawa mata ƴan NYSC alawus daga N33,000 zuwa N100,000.
Sanata Shehu Sani ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa ƙara alawi na matasa masu yi wa ƙasa hidima watau NYSC zuwa N77,000.
Sai dai ya ce ya kamata matasa mata masu yiwa kasa hidima su samu karin alawus fiye da maza saboda sun fi shan wahala a aikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ɗan majalisar tarayyan ya bayyana haka ne a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Tuwita ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, 2024.
Gwamnatin Tinubu ta ƙara alawin ƴan NYSC
Idan baku manta ba hukumar kula da matasa masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta sanar da ƙarin alawi daga N33,000 zuwa N77,000 kuma ya fara aiki daga watan Yuli.
A wata sanarwa da NYSC ta fitar a shafinta, ta ce hukumar albashi ta ƙasa ta aiko mata da takarda a hukumance game da ƙarin alawus din ƴan NYSC.
"N100,000 ya kamata a ba mata" - Shehu Sani
Da yake martani kan haka, Sanata Shehu Sani ya ce ƙarin abin a yaba ne amma ya kamata a banbanta alawus na mata da na maza a NYSC.
Shehu Sani ya ce:
"Ƙarin alawus na ƴan bautar ƙasa zuwa N77,000 abin a yaba ne, amma kamata ya yi ƙarin alawin mata ya kai N100,000 saboda sun fi shan wahala."
Gwamnatin Tinubu ta fara byan sabon albashi
A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000.
Hakan na zuwa ne watanni bakwai bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashin ma'aikatan gwamnati.
Asali: Legit.ng