Tsohon Kwamishina Ya Caccaki Gwamna Dauda, Ya Ba Shi Shawara kan Matawalle

Tsohon Kwamishina Ya Caccaki Gwamna Dauda, Ya Ba Shi Shawara kan Matawalle

  • Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar
  • Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda ya buƙaci Gwamna Dauda Lawal ya daina ɗora alhakin matsalar akan Bello Matawalle
  • Ya shawarce shi da ya haɗa kai da ƙaramin ministan na tsaro domin kawo kan matsalar ƴan bindigan da ta addabi jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya daina ɗora alhakin matsalar rashin tsaro kan Alhaji Bello Matawalle.

Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda ya buƙaci gwamnan da ya mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Tsohon kwamishina ya caccaki Gwamna Dauda
Tsohon kwamishinan Zamfara ya ba Gwmana Dauda shawara Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Juma’a, tsohon kwamishinan ya yi Allah wadai da kalaman da Gwamna Dauda Lawal ya ke yi kan Matawalle, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsohon dan majalisa ya ba Gwamna Dauda lakanin kawo karshen 'yan bindiga a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba Gwamna Dauda

Ya ce irin waɗannan kalamai da Gwamna Dauda Lawal ya yi a kafafen yaɗa labarai kan magabacinsa Matawalle, ba su da wani amfani ga ci gaban jihar.

Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoga ya ce dole gwamnan ya haɗa kai da Matawalle domin tunkarar ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

"Ya kamata shugabannin biyu su haɗa kai domin tabbatar da nasarar ayyukan yaƙi da ƴan bindiga da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi a jihar."
"Ina ganin ya kamata Gwamna Dauda Lawal ya dakatar da wasan ɗora alhaki kan batutuwan da ba su dace ba, ya maida hankali wajen ci gaban jihar."

- Alhaji Ibrahim Danmalikin-Gidangoda

A cewarsa, ya kamata a yaba wa Matawalle kan nasarorin da aka samu a baya-bayan nan a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga ba a Zamfara kaɗai ba har ma a yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Kungiya ta bayyana dalilin gwamnan Zamfara na tsoron Bello Matawalle

Ƙungiya na neman a dakatar da Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya a jam’iyyar APC ta Tinubu Youth Network (TYN), ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya daƙatar da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kungiyar ta kuma buƙaci shugaban ƙasan da ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan alaƙar Matawalle da ƴan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng