"An Yiwa Ƙasa Addu'a": Tinubu Ya Haɗu da Tsofaffin Shugabanni 2 da Sarki a Masallacin Jumu'a
- Bola Ahmed Tinubu ya gamu da Namadi Sambo da Abdulsalami Abubakar a Masallacin Juma'a a babbar birnin tarayya Abuja
- Kakakin majalisar wakilai da mai martaba Etsu na Nufe, Alhaji Yahaya Abubakar na cikin waɗanda suka yi sallah tare da Tinubu
- Manyan da sauran Musulmi da suka yi sallah a masallacin sun yi wa ƙasa addu'o'i yayin da take cika shekara 64 da samun ƴanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya haɗu da tsohon shugaba na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo a Abuja.
Manyan jiga-jigan sun haɗu da juna ne a wurin sallar Juma'a yau 27 ga watan Satumba, 2024 a babban birnin tarayya Abuja.
Mai ba shugaba Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka tare da hotuna a shafinsa na manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya yi Jumu'a tare da manya
Tun bayan sauka daga mulki, Namadi Sambo, tsohon mataimakin shugaban kasa a mulkin Jonathan, bai sake neman takara a siyasa ba, har yanzu yana nan a PDP.
Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas da Mai Martaba Etsu na Nufe, Alhaji Yahaya Abubakar na cikin waɗanda suka yi Sallah a Masallacin.
Shekara 64: An yiwa Najeriya addu'o'i
Tinubu da shugabannin da Musulmin da suka yi sallar Juma'a a Masallaci sun yi wa ƙasar nan addu'o'i yayin da take cika shekara 64 da samun ƴanci ranar 1 ga watan Oktoba.
A bisa al'ada Najeriya na shirya gagarumin biki a babban filin Eagle Square duk shekara domin murnar zagayowar ranar da ƙasar ta samu ƴanci kai daga turawa.
Sai dai a bana gwamnatin tarayya ta ce za a yi bikin ne saisa-saisa a ranar da Najeriya ta cika shekaru 64 duba da yanayin kunci da wahalar rayuwar da ake ciki.
Tinubu ya naɗa daraktoci 7 a NTA
A wani labarin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin manyan daraktoci bakwai a gidan taabijin na Najeriya (NTA)
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya sanar da haka ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng