Ana Shirin Korar Ministoci, Ministan Tinubu Ya Nada Hadimi, Ya Gargadi Yan Kwangila

Ana Shirin Korar Ministoci, Ministan Tinubu Ya Nada Hadimi, Ya Gargadi Yan Kwangila

  • Yayin da ake jita-jitar korar wasu Ministoci a gwamnatin Tinubu, Nyesom Wike ya nada hadimi na musamman
  • Ministan harkokin Abuja ya nada Dr. Samuel Atang a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren gudanarwa
  • Ministan ya kuma gargadi yan kwangila a birnin Abuja kan yawan samun jinkiri inda ya ce zai sallame su daga aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya nada sabon hadiminsa na musamman.

Nyesom Wike ya nada Dr Udo Samuel Atang a matsayin hadiminsa a bangaren gudanarwa.

Wike ya nada hadimi ana tafe radin sallamar Ministoci
Nyesom Wike ya yi barazana ga yan kwangila a Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Nyesom Wike ya nada hadimi na musamman

Sakataren yada labaransa, Anthony Ogunleye shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Talauci: Gwamnati ta kara ba yan kasa hakuri, Minista ya ce sauki na tafe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogunleye ya ce kafin nadin Samuel Atang ya rike muƙamin shugaban gudanarwa a hukumar FCTA.

Ya ce Atang ya ba da gudunmawa sosai da kawo cigaba yayin da yake shugabancin a hukumar FCTA.

Wike ya gargadi yan kwangila a Abuja

Wannan nadi na zuwa ne yayin da ake jita-jitar Bola Tinubu zai yi garambawul a majalisar ministoci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya shirya sallamar wasu daga ministoci domin kawo sababbin jini a gwamnatinsa domin inganta lamura.

Wata majiya ta tabbatarwa Punch cewa ana hasashen za a sallami Ministoci aƙalla 11 da wasu hadimai na musamman.

Ana cikin haka, Wike ya yi barazana ga yan kwangila da ke kawo cikas a gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Wike ya koka kan yadda ake samun jinkiri daga yan kwangilar inda ya ce ba zai daga musu kafa ba.

Kara karanta wannan

Zargin $49bn: Jonathan ya maidawa Sanusi II martani kan satar kudi a gwamnatinsa

Wike ya gana da majalisar PDP-BOT

Kun ji cewa Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya gana da ƴan majalisar amintattu na PDP (BoT) a daren ranar Talata, 17 ga watan Satumba 2024.

Rahotanni sun tabbatar da cewa taron, wani ɓangare ne a yunƙurin BoT na kawo ƙarshen rigimar siyasar da ta dabaibaye jihar Ribas.

Daga canjin gwamnati a Mayun 2023, Wike da magabacinsa, Siminalayi Fubara suka raba gari kan wanda zai zama jagoran PDP a jihar Ribas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.