Gwamnati Ta Raba Kanta da Rancen €64m da Ganduje Ya Laftowa Kano a 2018

Gwamnati Ta Raba Kanta da Rancen €64m da Ganduje Ya Laftowa Kano a 2018

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce babu gaskiya a cikin labarin cewa ta karbo rancen makudan kudi a waje
  • A makon nan ne aka rika yada cewa za a yi aikin ruwa a Kano da rancen Naira biliyan 177 da aka karbo daga Faransa
  • Ofishin kula da basussuka na Kano ya musanya cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tilowa Kano bashin kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta barranta kanta da rancen Naira biliyan 177 da gwamnatin Ganduje ta karbo daga Faransa a shekarar 2018.

A kwanan nan ne aka samu labarin gwamnatin Kano za ta kashe Naira miliyan 177 a kan harkar inganta ruwa da hadin gwiwar hukumar cigaban Faransa (FDA).

Kara karanta wannan

Bayan zarginta da jefa jama'a a wahala, gwamnati ta fadi alfanun cire tallafin fetur

Abba Kabir
Gwamnatin Kano ta dora rancen€64m kan gwamnatin Ganduje Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta tattaro cewa tun a zamanin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje jihar ta shiga yarjejeniyar da hukumar ta kasar Faransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Gwamnatin Abba ba ta ci bashi ba

Daraktan ofishin kula da basussuka na jihar Kano, Hamisu Hadi Ali ya ce da gangan ake yada labarin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta karbo aro.

Ya ce tun da gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau mulki, ba a taba rancen ko sisi ba daga ciki ko wajen kasar nan, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta wallafa.

"Ganduje ya bar Kano da bashi:" Gwamnati

Ofishin kula da basussuka na Kano ya ce tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta bar jihar luntsum cikin basussuka.

Daraktan ofishin, Hamisu Hadi Ali ya ce yanzu abin da ke gabansu shi ne biyan wadancan basussuka, inda ya ce daga rancen €64m da aka yi na aikin ruwa, har an fitar da €13m.

Kara karanta wannan

Talauci: Gwamnati ta kara ba yan kasa hakuri, Minista ya ce sauki na tafe

NNPP" Gwamnatin Kano ta karbi yan adawa

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin NNPP ta jihar Kano ta karbi dimbin yan wasu jam'iyyu biyu a jihar, inda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi maraba da su.

'Yan siyasar da su ka fito daga jam'iyyun NRM da ZLP sun ce ayyukan alheri da salon mulkin gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jawo hankalinsu zuwa NNPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.