"Ba Laifinsa ba ne”: Yakubu Dogara Ya Yi Maganar Tinubu da Cire Tallafin Fetur

"Ba Laifinsa ba ne”: Yakubu Dogara Ya Yi Maganar Tinubu da Cire Tallafin Fetur

  • Tsohon shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa babau laifin shugaba Bola Tinubu a cire tallafin mai
  • Rt. Hon. Dogara ya ce tun kafin hawan Tinubu mulki aka cire tallafin mai a Najeriya kawai shi ya tabbatar da haka ne a baki
  • Tsohon dan Majalisar ya koka kan yadda ake ce-ce-ku-ce game da matsalolin Najeriya a kullum ba tare da neman gyara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban Majalisar Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya yi magana kan cire tallafin mai a Najeriya.

Dogara ya ce ba Shugaba Bola Tinubu ba ne ya cire tallafin wanda ya jefa al'umma cikin mummunan yanayi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware N24bn domin ragewa talakawa radadi, an fadi yadda tsarin yake

Doraga ya magantu kan cire tallafin mai, ya ce ba laifin Tinubu ba ne
Hon. Yakubu Dogara ya kare Tinubu kan cire tallafin mai a Najeriya. Hoto: Hon. Yakubu Dogara.
Asali: Facebook

Dogara ya kare Tinubu kan cire tallafi

Tsohon kakakin Majalisar ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Juma'a 27 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogara ya ce tun kafin Tinubu ya ci zaben da aka gudanar a 2023 aka cire tallafin mai a Najeriya.

Ya ce tun kafin zaben Tinubu babu sashen biyan kudin tallafin mai a cikin kasafin shekarar 2023, Punch ta ruwaito.

"Cire tallafi ne abin da ya dace " - Dogara

Tsohon dan majalisar ya ce duk da yan Najeriya na jin jiki bayan cire tallafin amma hakan shi ne ya dace.

"Matsalar kasar nan shi ne kowa yana son fadin damuwarta amma ba a maganar yadda za a shawo kan matsalolin."
"Maganar tallafi babu shi a kasafin kudi, duk wanda ya ce maka Tinubu ne ya cire, wasa yake yi, babu yadda za a yi ya dakatar da abin da babu shi a kasafi."

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

"Gaskiya ita ce ba Tinubu ba ne ya cire tallafin mai kawai shi ne ya tabbatar da haka a baki."

Tinubu zai sake raba biliyoyi ga talakawa

Kun ji cewa yayin da ake cikin mawuyacin hali, gwamnatin Bola Tinubu ta sake ware N24bn domin rabawa gidajen talakawa.

Shirin zai shafi akalla gidaje 991,261 da ke jihohin Najeriya 36 da kuma birnin Abuja saboda ragewa al'umma radadi.

Wannan na zuwa ne bayan raba makudan kudi a watan Agustan da kuma farkon wannan wata na Satumbar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.