1 ga Oktoba: Masu Shirya Sabuwar Zanga Zanga Sun Aika Saƙo ga Ƴan Sandan Najeriya
- Masu shirya zanga-zanga a faɗin Najeriya ranar 1 ga watan Oktoba sun buƙaci tsaro daga rundunar ƴan sanda domin komai ya tafi lafiya
- Hakan na kunshe a wata sanarwar haɗin guiwa da ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar suka fitar, sun koka kan halin tsadar rayuwa
- Ƙungiyoyin sun koka kan yadda hauhawar farashi ke ƙaruwa sakamakon ƙarin farashin litar man fetur da aka yi kwanan nan a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Masu shirya zanga-zangar da za a yi ranar ƴancin kai watau 1 ga watan Oktoba, 2024 sun aika wasiƙa zuwa ga rundunar ƴan sandan Najeriya.
Masu shirya zanga-zangar kan tsadar rayuwa sun buƙaci rundunar ƴan sanda ta ba su kariya a lokacin da suka fito kan tituna domin nuna fushinsu kan halin da ake ciki.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwar haɗin guiwa da ƙungiyoyin ERC, MFC, YRC, JAF da PACOR suka fitar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan sun koka kan tsadar fetur
Kungiyoyin sun koka kan tashin farashin man fetur daga N200 a shekaru biyu da suka wuce zuwa N900 ko sama da haka a wasu sassan ƙasar nan.
Sun ƙara da cewa yunwa ta fara neman kai mutane kasa saboda tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki musamman abinci, Punch ta ruwaito.
A cewar ƙungiyoyin, a yanzu sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka amince da shi ba zai ragewa ma'aikatan gwamnati raɗaɗin komai ba.
Wannan dai na zuwa ne kusan watanni biyu bayan zanga-zangar da matasa suka yi a watan Agusta, wadda ta rikiɗa ta zama tashe-tashen hankula da sace-sace.
Yadda matasa suka shirya zanga-zanga
Amma a wannan karon za a yi zanga-zangar ne a ranar da Najeriya ke cika shekara 64 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Hassan Soweto, jagoran kungiyar ERC ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar cikin lumana don nuna adawa da "manufofin da suka kawo talauci"
Ya ce za su fara zanga-zanga a Legas da karfe 7:30 na safiya kuma za su haɗu a ƙarƙashin gadar Ikeja, inda za su bi tituna domin wayar da kan jama'a.
Masu shirya zanga-zanga sun jero buƙatu 17
A wani rahoton kuma matasan Najeriya na cigaba da shirye shiryen gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu.
A wannan karon, matasan sun fitar da wasu jerin bukatu 17 ɗa suke buƙatar gwamnatin tarayya ta cika musu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng