Ana Zaman Makoki a Borno: Ambaliya Ta Halaka Mutane 11,Ta Lalata Kadarori a Neja

Ana Zaman Makoki a Borno: Ambaliya Ta Halaka Mutane 11,Ta Lalata Kadarori a Neja

  • Ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Neja ta yi sanadiyar mutuwar mutane 11 da lalacewar makarantu 245, a cewar hukumar NSEMA
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Neja ta kuma ce ambaliyar ta shafi garuruwa 529 a a kananan hukumomi 19 cikin 25
  • Mamakon ruwan saman da ake tafkawa kamar yadda NiMet ta yi hasashe ya sanya Neja a jihohin da ke fuskantar barazanar ambaliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Neja ta yi karin haske kan asarar da jihar ta tafka a bana sakamakon ambaliyar ruwa.

Baya ga ruwan sama, hukumar ta lura da cewa ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon cika da batsewar madatsun ruwa daban-daban a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami’an gidan yari 4, ta fadi dalili

Hukumar NSEMA ta yi magana kan barnar da ambaliya ta yi a Neja
Neja: Mutane 11 sun mutu yayin da aka rasa kadarori masu yawa ambaliya. Hoto: Justin Sullivan
Asali: Getty Images

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Neja

Hukumar NSEMA ta kuma dora alhakin ambaliyar ga toshewar hanyoyin ruwa ta dalilin zubar da shara ba bisa ka'ida ba, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darakta Janar na NSEMA, Abdullahi Baba-Arah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Abdullahi Baba-Arah, ya ce rahoton na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar NSEMA da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ofishin ayyuka na Minna.

Shugaban ya bayyana cewa har yanzu jihar Neja na shan mamakon ruwan sama, don haka ne suke tunanin cewa:

"Ruwan saman da aka samu a bana kamar yadda NIMET ta yi hasashe ya sanya jihar Neja a cikin jihohin kasar nan da ambaliyar ta shafa.”

Mutane 11 sun mutu a ambaliyar Neja

A cewar shugaban NSEMA, mutane 11 ne suka halaka sakamakon ambaliyar a kananan hukumomi biyar da suka hada da Mokwa, Shiroro, Munya, Katcha da Rijau.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta mamaye makarantu da asibitoci, ruwa ya cinye kauyuka 82

Ya kuma kara da cewa akalla garuruwa 529 a cikin kananan hukumomi 19 cikin 25 da ke a jihar suka fuskanci ambaliyar ruwan.

Haka kuma, mutane 41,192 da gidaje 6865 abin ya shafa yayin da garuruwa 34 suka rasa gidajensu kuma a halin yanzu suke samun mafaka a cibiyiyon 'yan gudun hijira.

Mutanen Maiduguri na cikin garari bayan ambaliya

A wani rahoton, mun ruwauto cewa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri da ke jihar Borno sun bayyana halin kuncin da suka shiga na rashin muhalli.

Wasu da aka zanta da su kan halin da suke ciki, sun bayyana cewa yanzu sun koma kwana a kan tituna saboda ruwa ya lalata gidajensu kuma an rufe matsugunan gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.