Tinubu Zai Kori Gbajabiamila Ya Nada Ministan Buhari a Mamadinsa? Bayanai Sun Fito
- Shugaba Bola Tinubu na iya korar shugaban ma'aikan fadarsa, Femi Gbajabiamila, a wani yunkuri na yiwa majalisar ministocinsa garambawul
- Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa Tinubu ya rubuta sunan tsohon minista, Babatunde Fashola, a matsayin wanda zai gaji Gbajabiamila
- An kuma ruwaito cewa idan har Fashola ya ki amincewa da mukamin, to za a iya nada babban sakataren gwamnati, Hakeem Muri-Okunola
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu ya kori shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, bisa zargin rashin gudanar da aiki yadda ya kamata.
Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa tsohon kakakin majalisar tarayyar na daga cikin wadanda za su iya rasa mukamansu a garambawul din da Tinubu zai yi wa majalisar ministocinsa.
Wanene zai maye gurbin Gbajabiamila?
Majiyoyin sun ce Babatunde Fashola, tsohon ministan ayyuka a karkashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai maye gurbin Gbajabiamila, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan Fashola ya ki karbar mukamin, majiyoyin sun ce Tinubu ya rubuta sunan Hakeem Muri-Okunola, babban sakataren shugaban kasar na yanzu a matsayin magajin Gbajabiamila.
Rahoton jaridar ya bayyana cewa:
"Ana ganin Babatunde Fashola a matsayin wanda zai maye gurbin Gbajabiamila. Idan ya ki karbar tayin, babban sakataren shugaban kasa na yanzu, Hakeem Muri-Okunola zai samu mukamin."
Hasashen dawo da wasu ministocin Buhari
Rahoton ya ci gaba da cewa majiyoyin da ke da masaniya kan garambawul din sun ce akwai ministocin da za a sauyawa ma'aikatu yayin da wasu kuma za a sallame su.
Majiyoyin sun kuma yi nuni da cewa akwai wasu ministocin tsohuwar gwamnatin Buhari da a yanzu Tinubu ke so ya dawo da su domin yin aiki karkashinsa.
Shirin yi wa ministoci garambawul na zuwa ne watanni bayan da shugaban kasar ya cika shekara daya a ofis wanda ya sa 'yan Najeriya da dama neman a sauya tsarin gwamnati.
Yaushe Tinubu zai yi garambawul?
Tun da fari, mun ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Bola Tinubu zai yiwa majalisar ministocinsa garambawul na gaba kadan.
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa ya fayyace cewa babu wani kayyadadden lokacin da za a yi garambawul, amma tabbas za a yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng