Yan Najeriya Sun Fusata Da ‘Hamster Kombat’, Sun Yi Magana kan Kashi Na 2
- "Yan Najeriya sun yi Allah wadai da farashin 'Hamster Kombat' bayan ta fashe a yau Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024
- Wasu da dama sun koka tun farko kan yadda aka lissafa musu abin da suka samu wanda ya kashe musu guiwa a harkar
- Hakan na zuwa ne bayan shafe akalla watanni biyar ana 'mining' na 'Hamster Kombat' kafin shigarta kasuwa a Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
A yau Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024 aka sanar da fashewar 'Hamster Kombat' ga masu mining.
Bayan shafe watanni biyar ana 'mining', mutane da dama sun ji ajikinsu ganin yadda farashin ya fito.
Fashewar 'Hamster Kombat' ta zo da matsala
Sai dai tun farko, ganin yadda ake kawo wasu tsare-tsare da lissafe-lissafe ya kashewa mutane guiwa kafin sake ta a kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tunanin samun miliyoyin kudi sai ga shi wasu ana sallamarsu da $4 zuwa $7 wasu kuma kasa da haka.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin wadanda suka fi samun kudi su ne masu daloli bakwai zuwa 17.
Shafin 'Hamster Kombat' ya wallafa a manhajar X game da tabbatar da shi a kasuwa wanda mutane da dama suka yi ta tsokaci.
"Lokaci ya yi"
"An fara kasuwacin Hamster a hukumance, mu na taya ku murna."
- Cewar sanarwar
Martanin yan Najeriya game da 'Hamster Kombat':
Geoffrey Nwankpa:
"Kun ba ni dusa bayan shafe watanni hudu inda kashe hamster, beraye da zomaye ko kuma duk abin da ke kama da hamster."
realworldxxp:
"Dan uwa na wannan shi ne mafi lalacewar manhaja."
Obj:
"Kenan na shafe watanni biyar ina hakar hamster amma a saka min da wannan? da gaske ne"?
Legit Hausa ta ji bakin wasu game da 'Hamster Kombat'
Aisha Muhammad ta koka kan farashin inda ta ce su kam ko kyauta ba za su shiga kashi na biyu ba.
"Duk da ni daman ba wasu da yawa na tara ba amma gaskiya ban yi tsammanin haka ba, ganin yadda aka lissafa ta."
- Aisha Muhammad
Auwal Adamu M. ya ce yana hasashen kashi na biyu na 'Hamster Kombat' zai ba da mamaki inda ya karawa yan baiwa karfin guiwa.
Wata mai suna Jamila Muh'd Ali ta ce 'Hamster Kombat' sun yaudari al'umma amma za a koma wasu masu fashewa na kusa domin cin moriya.
An haramta 'mining' lokacin aiki a asibiti
Kun ji cewa Asibitin Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe ya haramtawa ma'aikata 'kirifto' da 'mining' yayin da suke bakin aiki.
Hukumomin suka ce sun dauki matakin ne domin kare faruwar salwantar da rayuwa saboda yadda lamarin ke dauke hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng