Sarki Sanusi II Ya Yiwa Jonathan Martani kan Tsige Shi daga Gwamnan CBN a 2013

Sarki Sanusi II Ya Yiwa Jonathan Martani kan Tsige Shi daga Gwamnan CBN a 2013

  • Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya ce ko kadan ba ya jin haushin tsohon shugaban kasa Godluck Jonathan kan abin da ya faru 2014
  • Muhammadu Sanuisi II ya nuni da cewa bai dauki tsohon shugaban da gaba ba duk da ya tsige shi daga gwamnan babban bankin Najeriya
  • Hakazalika, sarkin ya yi magana kan wadanda ke kawo cikas ga matatar man Dangote yayin da ta fara aikin tace danyen mai a Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya jaddada cewa babu wata kiyayya tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Muhammadu Sanusi II ya ce ko kadan bai kullaci Jonathan kan tsige shi daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a shekarar 2013 ba.

Kara karanta wannan

Jonathan ya ci gyaran Sanusi II, ya fadi dalilin dakatar da shi a CBN a 2014

Sarkin Kano, Sanusi II ya yiwa Jonathan martani kan tsige shi daga gwamnan CBN
Sarki Sanusi II ya ce ba ya gaba da Jonathan kan tsige shi daga gwamnan CBN. Hoto: @masarautarkano, @GEJonathan
Asali: Twitter

Sanusi II ya yiwa Jonathan martani

Bayanin Sanusi II na zuwa ne bayan Jonathan ya musanta zargin cewa dala biliyan 49.8 sun bace a lokacin da ya ke shugaban kasa, inji rahoton Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na san cewa kowa na so na yi martani amma ba zan yi ba. Lokacin da aka ce in fito in yi jawabi, na fada Sir D. Kusman cewa ba zan yi magana kan lamarin ba.
"Ina matukar girmama shugabana. Amma zan ce wani abu kadan. Na farko dai, ina ci gaba da girmama shugabana, Jonathan kuma babu kiyayyarsa ko ta wani a raina."

- A cewar Sarki Sanusi II.

Mai martaba ya yi nuni da cewa lokacin da aka tsige shi daga gwamnan CBN ya zama sarki, bayan an tube rawaninsa ne ya ya samu matakin karatun PhD inda kuma yanzu ya ke kan kujerar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Zargin $49bn: Jonathan ya maidawa Sanusi II martani kan satar kudi a gwamnatinsa

Sarki ya magantu kan matatar Dangote

Sarkin na Kano ya kuma ce wasu masu hannu da shuni, wadanda suke samun arziki daga shigo da mai cikin kasar na kawo cikas ga matatar Dangote.

"Me zai sa har wani ya dakatar da mu daga sarra fetur da kanmu? Ba zai wuce saboda akwai masu hannu da shuni da ke samun arziki daga ci gaba da shigo da man ba.
"Wacce hanya za mu bi mu ganar da Najeriya cewa ita kasa ce da ke wakiltar jama'a ba wai kasar da wasu tsirarun masu mulki juya akalarta ba.? Wannan darasi ne babba."

Jonathan ya ci gyaran Sanusi II

A wani labarin mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce akwai kuskure cikin bayanin da Sanusi II ya yi kan dalilin sauke shi daga gwamnan Bankin CBN.

A yayin da ya ke jawabi a wani taron kaddamar da littafi a Abuja, Jonathan ya ce ko kadan ba maganar batan $49.8b ba ce ta saka ya dakatar da Sanusi II ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.