Tinubu Ya Ware N24bn domin Ragewa Talakawa Radadi, an Fadi Yadda Tsarin Yake

Tinubu Ya Ware N24bn domin Ragewa Talakawa Radadi, an Fadi Yadda Tsarin Yake

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali, Gwamnatin Bola Tinubu ta sake ware N24bn domin rabawa gidajen talakawa
  • Shirin zai shafi akalla gidaje 991,261 da ke jihohin Najeriya 36 da kuma birnin Abuja saboda ragewa al'umma radadi
  • Wannan na zuwa ne bayan raba makudan kudi a watan Agustan da kuma farkon wannan wata na Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ware N24bn domin rabawa gidaje 991,261 a jihohi 36 na Najeriya.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne domin ragewa al'umma halin kunci da suke ciki a kasar.

Gwamnatin Tinubu ta ware N24bn domin tallafawa talakawa
Yayin da ake halin kunci, Gwamnatin Bola Tinubu za ta gwangwaje talakawa da biliyoyin nairori. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu zai sake tallafawa talakawa da kudi

Mai kula da hukumar NSIPA, Dr. Badamasi Lawal shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da jaridar The Guardian ta samu.

Kara karanta wannan

Ranar 'yanci: Gwamnatin Tinubu ta lissafa muhimman ayyukan da ta yiwa talakawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawal ya ce hakan na daga tsarin cigaba da biyan kudi har N3bn a watan Agusta da kuma N20bn a farkon watan Satumbar 2024.

Ya ce an kaddamar da shirin ne domin saukakawa al'umma halin matsin tattalin arziki da suke ciki.

Yadda tallafin zai taimakawa marasa karfi

Tallafin zai taimakawa gidaje musamman wadanda suke cikin wani hali domin rage musu radadin da suke ciki.

Har ila yau, Lawal ya ce tallafin zai taimaka musu wurin inganta lafiyarsu da kuma samar musu da abinci.

Lawal ya ce a watan Agustan 2024 an ware N3.8bn ga gidaje fiye da 150,000 yayin da a farkon watan Satumbar 2024 aka ware N20.9bn ga gidaje fiye da 80,000.

Wannan na zuwa yayin al'umma suka shiga mummunan yanayi na tsadar rayuwa a fadin kasar.

Tinubu ya magantu kan shigo da abinci

Kara karanta wannan

'Bai kamata ba': Gwamnatin Tinubu ta yi fatali da shigo da abinci, ta nemo mafita ga talaka

A wani labarin, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fadi shirinta na dakile shigo da kayan abinci daga ketare domin bunkasa tattalin arziki.

Ministan kudi, Mr. Wale Edun ya tabbatar da cewa gwamnatin ta dauki matakan hana shigo da abinci domin wadata Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cikin halin tsadar rayuwa musamman kayan abinci da dan Adam ya dogara da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.