Sanusi II Ya Amsa Kiran Girmama Manzon Allah SAW, Ya Cire Dardumar da Ta Tada Kura

Sanusi II Ya Amsa Kiran Girmama Manzon Allah SAW, Ya Cire Dardumar da Ta Tada Kura

  • Biyo bayan ce-ce-ku-ce da aka rika yi kan wata darduma a fadar sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sarkin ya saurari al'umma
  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya cire dardumar ne mai dauke da suna irin na Annabi Muhammadu SAW da ake zargin ana taka ta
  • Malaman addini da al'ummar Musulmi masu amfani da kafafen sadarwa sun yawaita kira ga sarkin kan cire dardumar domin ladabi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Kura ta lafa kan rigimar da aka yi a kan wata darduma da sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi amfani da ita.

Rahotanni sun nuna cewa sarkin ya cire dardumar duk da cewa ya yi karin haske kan dalilan amfani da ita.

Kara karanta wannan

An Saka Sarki Sanusi II a gaba kan zargin rashin girmama Annabi Muhammad SAW

Sanusi II
Sanusi II ya cire darduma mai sunan 'Muhammadu' a fadarsa. Hoto: Rahama Abdulmajid
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da hadimar shugaban kasa Bola Tinubu, Rahama Abdulmajid ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dardumar da ta tayar da kura a Kano

Legit ta ruwaito cewa al'umma sun tayar da kura a kafafen sadarwa bayan hango wata darduma da ake takawa mai dauke da sunan 'Muhammadu' a fadar Sanusi II.

Al'umma da dama ciki har da malaman addini sun soki sarkin kan amfani da dardumar inda suka ce bai girmama sunan 'Muhammadu' ba.

Sarki Sanusi II ya amsa kiran al'umma

Biyo bayan ce-ce-ku-ce da aka samu a kan dardumar, Sarki Muhammadu Sanusi II ya cire ta a fadarsa.

Al'umma da dama sun nuna farin ciki kan amsa kiran da sarkin ya yi na cire dardumar cikinsu har da hadimar Bola Tinubu, Rahama Abdulmajid.

Ga abin da ta wallafa:

Kara karanta wannan

Dakaru sun kara yin gagarumar nasara, sojoji sun hallaka abokin Bello Turji

Labari mai dadin ji. Allah Ya kara wa sarki lafiya da fadin kirji na karban kukan al'ummarsa.
Allah Ya kara wa Annabi SALLALLAHU ALAIHI wa sallam daraja

-Rahama Abdulmajid, hadimar Bola Tinubu

Sanusi II ya yi magana kan matsin tattali

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ce duka ƙalubalen da suka addabi Najeriya za a iya shawo kansu idan aka jajirce.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar gwamnatin Kano a fadarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng