Naira Ta Kara Rikitowa Ƙasa, Dala Ta Kuma Tashi a Kasuwar Canji a Najeriya

Naira Ta Kara Rikitowa Ƙasa, Dala Ta Kuma Tashi a Kasuwar Canji a Najeriya

  • Ƙimar datajar Naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar hada-hadar musaya ta ƴan canji ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024
  • Bayanai sun nuna Dalar Amurka ta ƙara tashi zuwa N1,680 daga N1,655 da aka yi cinikayya ranar Talata
  • Wani ɗan canji ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan makon da ke dab da ƙarewa bai yi wa Naira daɗi ba, inda ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kuɗin Najeriya watau Naira ta sake faɗuwa a kasuwar hada-hadar kuɗi ta bayan fage wadda aka fi sani da kasuwar ƴan canji jiya Laraba, 25 ga watan Satumba.

Bayanai sun nuna Dala ta ƙara tsada zuwa N1,680 daga farashin N1,655 da aka yi canjin kowace Dalar Amurka ɗaya a ranar Talata da ta wuce.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojoji suka hallaka shugabannin 'yan ta'adda 65

Naira da Dala.
Naira ta kara faɗuwa a kasuwar bayan fage, ta koma N1680 Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Darajar Naira ta ragu a farashin gwamnati

Har ila yau, Dalar Amurka ta sake ruguza Naira a farashin gwamnati ranar Laraba, inda aka yi cinikinta kan N1,667.4, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa farashin canji na kasuwar gwamnati NAFEM ya tashi zuwa N1,667.42 kan kowace dala daga N1,658.48/1$ a ranar Talata.

Hakan na nuni da cewa darajar Naira a farashin gwamnati ya ragu da N8.94 a jiya Laraba.

Bugu da ƙari, adadin Dalolin da aka yi ciniki a kasuwar hukuma ya ragu da kashi 39.6% zuwa Dala miliyan 100.47 daga Dala miliyan 166.36 da aka yi ciniki ranar Talata.

Bisa haka tazarar da ke tsakanin farashin Dala a kasuwar ƴan canji da farashin gwamnati ya ƙaru zuwa N12.58 daga N3.48.

'Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki'

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mai hada-hadar canji a kasuwar bayan fage kuma ya tabbatar da cewa baki ɗaya wannan makon bai yi wa Naira kyau ba.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ba zabaɓben gwamnan jihar Edo takarda shaida, bayanai sun fito

Muhammad Abba ya shaidawa wakilinmu cewa a yanzu Dala ɗaya ta kusa rufe N1,700, kuma matuƙar ba a ɗauki mataki ba, to haka za ta ci gaba da tashi.

A kalamansa ya ce:

"Idan ka duba daga ranar Litinin zuwa yau, Dala ta tashi sosai, a rana ɗaya za ka ga ta karu da N15 zuwa N30, idan kuma aka yi sa'a Naira ta farfaɗo, za ka ga ba zai wuce da N3, N5 zuwa N10 ba."

CBN ya koka da gwamnatin Buhari

A wani rahoton gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Olayemi Cardoso ya yi magana kan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a Najeriya.

Olayemi Cardoso ya ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tattalin arziki ne da ya riga ya ruguje kuma yana kan gyara ne a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262