Ranar 'Yanci: Gwamnatin Tinubu Ta Lissafa Muhimman Ayyukan da Ta Yiwa Talakawa

Ranar 'Yanci: Gwamnatin Tinubu Ta Lissafa Muhimman Ayyukan da Ta Yiwa Talakawa

A yayin da ake shirye shiryen murnar ranar yancin Najeriya a Oktoba, gwamnatin Bola Tinubu ta lissafa cigaban da ta kawo ga yan kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin muhimman ayyuka da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi a Najeriya.

Gwamnatin ta fitar da ayyukan ne domin shirin bikin ranar yancin Najeriya da za a yi a 1 ga watan Oktoba.

Tinubu
An lissafa manyan ayyukan Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya lissafa ayyukan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin ayyukan da Tinubu ya yi a Najeriya

Kara karanta wannan

Talauci: Gwamnati ta kara ba yan kasa hakuri, Minista ya ce sauki na tafe

1. Samar da motocin CNG

Sanata George Akume ya ce gwamnatin tarayya ta samar da kayan canza motoci daga amfani da man fetur zuwa iskar gas ta CNG a kyauta.

Hakan na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi da ya jawo tashin farashin kudin man fetur a Najeriya.

2. Rabon tallafin gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta kawo shirin ba al'umma tallafi domin rage radadi.

3. Karin albashi

Sanata George Akume ya ce gwamnatin tarayya ta amince da karin mafi albashin ma'aikata zuwa N70,000 a Najeriya.

4. Samar da lamunin karatu

Akume ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ba dalibai sama da 22,120 lamunin karatu har N2.5bn.

5. Yaki da yan ta'adda

Cikin nasarori, Sanata George Akume ya ce gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen yakar yan ta'adda inda a yanzu ake kashe manyan yan bindiga.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

6. Magance ambaliyar ruwa

Sanata George Akume ya ce Bola Tinubu ya dauki matakan da za su hana faruwar ambaliyar ruwa a Najeriya da aka yi fama da ita a bana.

A ƙarshe, sakataren gwamnatin ya ce Bola Tinubu yana sane da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriya kuma yana ɗaukan matakan sa suka dace.

Tinubu zai fadada kofofin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta fitar da sanarwa kan wasu tsare tsare da ta kawo a kan tattalin arzikin Najeriya.

Hadimin shugaban kasa a kan tsare-tsaren haraji, Taiwo Oyedele ne ya fitar da sanarwar kan yadda sabon tsarin zai fara aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng