'Bai Kamata ba': Gwamnatin Tinubu Ta Yi Fatali da Shigo da Abinci, Ta Nemo Mafita ga Talaka
- Gwamnatin Bola Tinubu ta fadi shirinta na dakile shigo da kayan abinci daga ketare domin bunkasa tattalin arziki
- Ministan kudi, Wale Edun ya tabbatar da cewa gwamnatin ta dauki matakan hana shigo da abinci domin wadata Najeriya
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cikin halin tsadar rayuwa musamman kayan abinci da dan Adam ya dogara da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fadi aniyarta wurin dakile shigo da kayan abinci daga ƙasashen ketare domin wadatarshi a gida Najeriya.
Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun ya ce gwamnatin ta rage yawan shigo da abinci domin bunkasa tattalin arzikin cikin gida.
'Amfanin hana shigo da abinci' - Gwamnatin Tinubu
Edun ya fadi haka ne yayin wani taro a Abuja a yau Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya ce dakile yawan shigo da abinci daga ketare zai bunkasa harkokin noma da kuma samar da wadataccen abinci.
"Bai kamata mu na shigo da abinci daga waje ba, dole ne mu tabbatar Najeriya ta dogara da kanta domin samun cigaba."
"Yana da muhimmanci mu kiyaye kawo cikas a samar da abinci a gida, bai kamata mu cika kasuwanninmu da kayan abinci daga ketare ba."
- Wale Edun
Gwamnatin Tinubu ta shirya bunkasa harkokin noma
Ministan ya ce gwamnatinsu ta himmatu wurin samar da tallafi ga ƙananan manoma domin bunkasa harkokin gona.
Daga cikin kayayyakin da za a tallafawa manoman sun hada da takin zamani da iri da na'urorin ban ruwa da sauransu.
Tinubu ya shirya sallamar wasu Ministoci
Kun ji cewa yan siyasa da dama sun fara kama kafa tun bayan fitar da rahoto cewa Bola Tinubu ya shirya sallamar wasu ministocinsa.
Wasu daga cikinsu sun fara neman yadda za a yi yaransu su tsallake wannan sauye-sauye da za a yi a gwamnatin Tinubu.
Hakan ya biyo bayan samun labarin cewa shugaban zai yi garambawul domin kawo wasu sababbin jini a mukaman Ministoci a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng