Gwamna Ya Kaɗu da Tashin Fetur, Ya Ba da Umarnin Sauko da Kudin Lita daga N2500
- Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya kafa kwamiti na musamman bayan tashin farashin litar mai har N2,500
- Umo Eno ya dauki matakin ne domin sanya ido kan hada-hadar fetur a Akwa Ibom bayan samun matsala da dillalai
- Hakan ya biyo bayan janye samar da mai da dillalan karkashin kungiyar IPMAN suka yi da ya tilasta tashin farashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta kafa kwamitin kula da hada-hadar man fetur.
Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan siyar da litar mai kan N2,500 a wurare da yawa da ke fadin jihar.
Farashin fetur: Gwamna ya kafa kwamiti
Sakataren gwamnatin jihar, Enobong Uwah shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a jiya Laraba 25 ga watan Satumbar 2024, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kafa kwamitin domin kula da hada-hadar man bayan tashin farashin saboda rikici tsakanin kungiyar dillalan man da kuma hukumar tsaro.
Leadership ta ce tsohon dan majalisa, Godwin Ekpo shi zai jagoranci kwamitin mai dauke da mambobi 13 domin gudanar da aikin.
Musabbabin kafa kwamiti a Akwa Ibom
Kafa kwamitin na zuwa ne awanni 24 bayan Gwamna Umo Eno ya gana da mambobin kungiyar IPMAN.
Hakan ya biyo bayan janye samar da mai din da IPMAN ta yi wanda ya tilasta tashin farashin litar mai har N2,500.
Dillalan man sun umarci mambobinsu da su rufe gidajen mai bayan zargin kwace manyan motocin mambobinsu.
Umarnin da ya fara aiki a ranar Talata 24 ga watan Satumbar 2024 ya kawo cikas ga harkokin sufuri da tsadar mai.
Dangote vs NNPCL: Tinubu ba zai tsoma baki ba
Kun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana kan rigimar da ke faruwa tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Aliko Dangote.
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ba zai tsoma baki kan rigimar da ke faruwa tsakaninsu ba saboda suna cin gashin kansu ne.
Wannan na zuwa ne yayin da aka fara takun-saka tsakanin kamfanonin guda biyu tun bayan Dangote ya fara fitar da mai a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng