Zaben Kananan Hukumomin Kano: Kotu Ta Dauki Mataki kan Bukatar Jam'iyyar APC

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Kotu Ta Dauki Mataki kan Bukatar Jam'iyyar APC

  • Babbar kotun tarayya da ke Kano ta ƙi amincewa da buƙatar APC na neman a dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar
  • APC ta shigar da ƙara tana neman kotun ta hana hukumar KANSIEC gudanar da zaɓen wanda za a yi a cikin watan Oktoba
  • Alƙalin kotun, mai shari'a Simon Amobeda ya kuma ɗage sauraron shari'ar har zuwa ranar, 4 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya da ke Kano ta ƙi amincewa da buƙatar da Jam’iyyar APC ta shigar kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

APC ta buƙaci kotun ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar 26 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ba zabaɓben gwamnan jihar Edo takarda shaida, bayanai sun fito

Kotu ta ki amincewa da bukatar APC a Kano
Kotu ta ki amincewa da bukatar APC kan zaben kananan hukumomin Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jam'iyyar APC ta shigar da ƙara a Kano

Masu shigar da ƙarar, Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC ta hannun lauyansu, Mustapha Idris, sun shigar da ƙorafi a ranar 18 ga watan Satumba tare da gabatar da ita a ranar 20 ga watan Satumba, cewar rahoton jaridar PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu shigar da ƙarar na neman kotu da ta hana hukumar KANSIEC gudanar da zaɓukan tare da bayar da umarni ga dukkanin ɓangarorin da su bar abubuwa a yadda suke.

Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da KANSIEC, majalisar dokokin jihar Kano, Antoni Janar na Kano, INEC, DSS, kwamishinan ƴan sandan Kano da kwamandan NSCDC na jihar.

Sauran sun haɗa da Anas Muhammad-Mustapha, Farfesa Sani Lawal-Malumfashi, Mukhtar Garba-Dandago, Isyaku Kunya, Shehu Kura, Kabiru Zakirai da Aminu Inuwa-Fagge.

Meyasa kotu ta yi watsi da buƙatar APC?

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC ta tsunduma yajin aiki, an samu bayanai

Mai shari’a Simon Amobeda, ya ƙi amincewa da buƙatar inda ya ce za a sanar da waɗanda ake ƙara domin su kawo dalilin da zai sa ba za a amince da buƙatar ba.

Kotun ta kuma amince da a gaggauta sauraran ƙarar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Mai shari'a Simon Amobeda ya kuma ɗage shari'ar har zuwa ranar, 4 ga watan Oktoban 2024 domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Shirin APC kan zaɓen ciyamomin Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana cewa a shirye take domin tunkarar zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi.

Shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa za su tabbatar da cewa ba a yi musu aringizon ƙuri'u ba a zaɓen na ranar, 24 ga watan Oktoban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng