Kungiyar NLC Ta Tsunduma Yajin Aiki, an Samu Bayanai

Kungiyar NLC Ta Tsunduma Yajin Aiki, an Samu Bayanai

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Akwa Ibom ta fara yajin aiki a faɗin jihar da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
  • NLC ta umarci ma'aikatan gwamnatin jihar da su dakatar da gudanar da ayyukansu daga Alhamis, 26 ga watan Satumban 2024
  • Shugaban NLC na jihar ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne sakamakon tashin gwauron zaɓin da farashin man fetur ya yi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Akwa Ibom ta tsunduma yajin aiki a faɗin jihar.

Ƙungiyar NLC ta umarci ma'aikatan gwamnatin jihar da su dakatar da gudanar da ayyukansu daga ranar Alhamis, 26 ga watan Satumban 2024.

Kara karanta wannan

Kungiya ta bayyana dalilin gwamnan Zamfara na tsoron Bello Matawalle

NLC ta shiga yajin aiki a Akwa Ibom
Kungiyar NLC ta fara yajin aiki a jihar Akwa Ibom Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƙungiyar ta shiga yajin aikin ne saboda wahalar da ma'aikata ke sha sakamakon tashin farashin fetur wanda ya kai N2,500 kan kowace lita ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fetur ya yi tsada a Akwa Ibom

A ranar Talata, 23 ga watan Satumba ƙungiyar dillalan mai ta IPMAN domin nuna goyon baya ga ƙungiyar direbobin tankokin mai ta kulle kusan dukkanin gidajen mai wanda hakan ya sanya farashinsa ya ƙaro da kaso 200%.

Shugaban IPMAN na jihar, Kwamared Francis Udoyen, ya yi bayanin cewa sun ɗauki matakin ne domin nuna goyon baya ga direbobin biyo bayan ƙwace tankokinsu ɗauke da mai da sojoji suka yi bisa zargin suna fasaƙwaurin man.

Gwamnan jihar Akwa Ibom ya yi alƙawarin shiga tsakani kan lamarin, tare da gargaɗin ɗaukar mataki kan masu sayar man fetur fiye da farashinsa na kasuwa.

Kara karanta wannan

Ana batun zaben Edo, an fara shirin dakatar da gwamna daga jam'iyya

Meyasa NLC ta shiga yajin aikin?

Shugaban NLC na jihar, Kwamared Sunny James ya nuna ɓacin ransa kan cewa duk da alƙawarin da gwamnan ya ɗauka har yanzu babu abin da ya sauya yayin da mutane ke ci gaba da shan baƙar wuya.

Ya bayyana cewa hakan ya sanya ya kira taron gaggawa na shugabannin ƙungiyar inda suka cimma matsayar fara yajin aikin.

"An umarci ma'aikata da su zauna a gidajensu daga daren ranar Laraba sakamakon ƙarin kuɗin fetur."
"An ɗauki wannan matakin ne domin nuna adawa da ƙarin kuɗin fetur da yadda zai yi tasiri kan rayuwar ma'aikata da sauran jama'a."

- Kwamared Sunny James

Karanta wasu labaran kan ƙungiyar NLC

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin tarayya sabon wa'adi, ta kafa sharadi

Jami'an DSS sun cafke shugaban NLC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun cafke shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero.

Jami'an na hukumar DSS sun cafke Joe Ajaero ne da safiyar ranar Litinin, 9 ga watan Satumban 2024 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng