'Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Gona, Sun Sace Mutum 6
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun farmaki wasu manoma suna tsaka da gudanar da aiki a gona a jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindigan sun sace mutane a harin da suka kai a ƙauyen Gidan Busa da ke ƙaramar hukumar Kachia
- Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu shanu masu yawa a wata rugar Fulani da ke makwabtaka da ƙauyen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wasu miyagun ƴan bindiga sun sace wasu manoma shida a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun sace manoman ne da suka haɗa da maza huɗu da mata biyu a ƙauyen Gidan Busa da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Wani shugaban al’ummar yankin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga jaridar Daily Trust a ranar Laraba ya ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce manoman na aiki gonakinsu ne a lokacin da ƴan bindigar ɗauke da makamai suka far musu.
Ya bayyana cewa ya sanar da wasu ƴan banga da ke ƙauyen Jobgwom wanda ke makwabtaka da su, waɗanda suka yi jerin gwano zuwa cikin dajin.
Ana fama da hare-haren ƴan bindiga
Shugaban al’ummar ya kuma bayyana cewa a ranar ne wasu ƴan bindiga suka kai hari a wata rugar Fulani a Gadan-Malam Maman da ke makwabtaka da su inda suka yi awon gaba da wasu shanu.
Ya ce ƴan bindigan da suka mamaye ƙauyen ɗauke da makamai, sun harbe wasu mutanen ƙauyen biyu tare da raunata su, yayin da suke tserewa da shanun da suka sace.
Shugaban al'ummar ya ƙara da cewa an sanar da sojojin halin da ake ciki kan lamarin.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba kan hare-haren da ƴan bindigan suka kai a ƙauyukan guda biyu.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, ya ci tura a yanzu.
Ƴan bindiga sun ƙona gidan mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan kungiyar aware ne (IPOB) sun bankawa gidan man Pinnacle wuta a jihar Enugu.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Jumu'a, 20 ga watan Satumba, 2024 a titin Agbani da ke cikin birnin Enugu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng