Kungiya Ta Bayyana Dalilin Gwamnan Zamfara Na Tsoron Bello Matawalle
- Ƙungiyar NYA ta yi magana kan cacar bakin da aka daɗe ana yi tsakanin gwamnan Zamfara da ƙaramin ministan tsaro
- NYA ta bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal yana tsoron Bello Matawalle ne saboda biyayyar da yake yi wa shugaba Bola Tinubu
- Ta shawarci gwamnan kan ya daina saka siyasa a cikin al'amuran rashin tsaro a Zamfara domin kare rayukan al'ummar jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wata ƙungiya mai suna Northern Youths Awareness (NYA) ta yi magana kan taƙaddamar gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da Bello Matawalle.
Ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa Gwamna Dauda Lawal, yana jin tsoron ƙaramin ministan tsaron ne saboda batun babban zaɓen 2027 da ke tafe.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba ta hannun jagoranta na ƙasa, Mustapha Gaya, NYA ta zargi Gwamna Dauda da nuna fargaba kan ƙaruwar tasirin Matawalle a yankin Arewa, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamna Dauda ke tsoron Matawalle?
Mustapha Gaya ya yi iƙirarin cewa Gwamna Dauda ya tsorata kan biyayyar da Matawalle ke yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma ɗaukakar da yake ƙara samu a yankin Arewa, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
"Biyayyar Matawalle ga Shugaba Tinubu ta sanya Gwamna Dauda cikin damuwa, wanda a yanzu ƴan adawa ke amfani da shi wajen haifar da ruɗani a Zamfara."
- Mustapha Gaya
Ya ci gaba da cewa tasirin Matawalle a siyasance a Arewacin Najeriya ya zama babban ƙalubale ga Gwamna Dauda Lawal da kuma burin jam’iyyar PDP gabanin zaɓen 2027.
An ba Gwamna Dauda shawara
A cewarsa, yanayin siyasar Zamfara ya ƙara dagulewa sakamakon zargin da ya alaƙanta Gwamna Dauda da ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
"Ba ya son ministan ya tona masa asiri, amma hakan ba zai magance masa matsalolinsa ba."
"Shawarar da zan ba shi ita ce ka da ya saka siyasa cikin matsalar rashin tsaro saboda rayukan al'ummar Zamfara."
- Mustapha Gaya
Karanta wasu labaran kan taƙaddamar Matawalle da Dauda
- Daukar nauyin 'yan bindiga: Gwamna Dauda ya dauki mataki kan Matawalle
- Matawalle ya fadi yadda ya kwaci Dauda Lawal daga hannun EFCC, ya kalubalance shi
- Matawalle ya yi wa gwamna Dauda martani kan zargin daukar nauyin 'yan bindiga
Matawalle ya magantu kan sulhu da ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan sulhun da ya yi da ƴan bindiga a lokacin da yake gwamnan Zamfara.
Matawalle ya bayyana cewa ya yi sulhu da ƴan bindigan ne da zuciya ɗaya domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng