N177.4bn: Shekarun Rashin Ruwa a Kano zai Zo Ƙarshe, Gwamnati na Aiki da Kasar Turai
- Gwamnatin Kano ta shiga jerin jihohin kasar nan da ke aiki da hukumar cigaban Faransa kan matsalar ruwa
- Yanzu haka ana taro bitar matakan da aka fitar a Kano, inda gwamna Abba Kabir ya ce za kashe biliyoyin Naira
- Bayan Kano, sauran jihohin da ke halartar taron a jihar sun hada da Filato, Osun, Ogun da Enugu don inganta ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce da gaske ta ke son kawo karshen matsalar ruwa a jihar.
Gwamnatin ta yi hadin gwiwa da hukumar cigaban Faransa (FDA) domin gudanar da ayyukan da za su magance matsalar ruwa da ta ki ci ta ki cinyewa.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa yanzu haka ana gudanar da taron jihohin da suka ci gajiyar ayyukan inganta bangaren ruwa na AFD a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano za ta samar da ruwa
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa jihar na bukatar shirin hadin gwiwa da AFD saboda yawa da bukatar ingantaccen ruwan sha a birni da karkara.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya fadi haka a ranar Laraba yayin taron jihohin da ke aikin da FDA da su ka hada da Filato, Ondo, Enugu da Osun.
Aikin ruwa a Kano zai lakume biliyoyi
Gwamnatin Kano ta ce aikin hadin gwiwa da ta ke yi da hukumar FDA zai lakume akalla Naira biliyan 177.4 don ruwan ya wadata.
Kwamishinan albarkatun ruwa, Ali Haruna Makoda da ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf a taron, ya ce za a kara wurin tunkodo ruwa a madatsar Tamburawa.
Gwamnatin Kano ta ware N2.5bn na aikin ruwa
A baya kun ji cewa gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 2.5 domin aikin ruwan madatsar Kafin Ciri domin karfafa noman yari a yankin da ke karamar hukumar Garko.
Shugaban shirin a Kano, Ibrahim Garba Muhammad ya ce aikin zai zo ne ta karkashin shirin gwamnati na habaka noma da kiwo (KSADP) da sauran tallafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng