Daga Karshe Matawalle Ya Fadi Dalilin Yin Sulhu da 'Yan Bindiga a Zamfara

Daga Karshe Matawalle Ya Fadi Dalilin Yin Sulhu da 'Yan Bindiga a Zamfara

  • Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan dalilinsa na yin sulhu da ƴan bindiga lokacin da yake mulkin jihar Zamfara
  • Matawalle ya bayyana cewa ya yi sulhu da ƴan bindigan ne da zuciya ɗaya domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar
  • Matawalle ya yi nuni da cewa sulhun da ya yi da ƴan bindigan ya sanya an samu tarin nasarori masu yawa a ɓangaren matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan sulhun da ya yi da ƴan bindiga a lokacin da yake gwamnan Zamfara.

Bello Matawalle ya kare matakin da ya ɗauka na yin sulhu da ƴan bindigan a lokacin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin 'yan bindiga: Gwamna Dauda ya dauki mataki kan Matawalle

Matawalle ya magantu kan sulhu da 'yan bindiga
Matawalle ya fadi dalilinsa na yin sulhu da 'yan bindiga Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Twitter

Idan dai za a iya tunawa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya zargi Matawalle da ɗaukar nauyin ƴan bindiga tare da ba su mafaka a gidan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Matawalle ya yi sulhu da ƴan bindiga?

Amma da yake mayar da martani yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Tv a ranar Talata, Mattawalle ya musanta zargin da gwamnan ya yi masa.

Matawalle ya bayyana cewa ya yi sulhu da ƴan bindigan ne da zuciya ɗaya domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Tsohon gwamnan na Zamfara ya bayyana cewa kafin ya yi sulhun da ƴan bindigan sai da ya tattaunan da dukkanin masu ruwa da tsaki na jihar.

Ya bayyana cewa sulhun da aka yi da ƴan bindigan ya sanya an samu zaman lafiya tare da kwato makamai da alburusai daga hannun ƴan ta’addan.

Kara karanta wannan

"Sama da mutum miliyan 88 na fama da talauci," Sheikh Pantami ya ba matasa mafita

"Mun samu nasarori sosai, mun ƙwato makamai masu yawa, mun ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su."

- Bello Matawalle

Gwamna Dauda ya magantu kan zargin Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamna Dauda Lawal, ya ce Nuhu Ribadu, da shugaba Bola Tinubu, suna sane da zargin da ake yi wa Bello Matawalle na alaƙa da bindiga.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ƙara da cewa ya kai rahoton ministan ga NSA da shugaban ƙasa tare da gabatar musu da wasu hujjoji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng