Ta tabbata: Tinubu Zai Yiwa Majalisar Ministoci Garambawul, Za a Runtuma Kora

Ta tabbata: Tinubu Zai Yiwa Majalisar Ministoci Garambawul, Za a Runtuma Kora

  • Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa nan ba da jumawa ba za a yi wa majalisar ministocin tarayya garambawul
  • Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, shine ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba, 25 ga Satumba
  • Onanuga ya ce watakila a yi garambawul din kafin 1 ga watan Oktoba ko bayan hakan, yayin da Tinubu ya yi kira ga ministocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yayin da jita jita ta yawaita kan makomar ministocin Najeriya, yanzu dai ta tabbata shugaba Bola Tinubu zai yiwa majalisar ministoci garambawul.

Fadar shugaban kasa ce ta tabbatar da wannan ci gaba inda ta alamta cewa babu abin da zai dakatar da Tinubu daga yiwa majalisar garambawul.

Kara karanta wannan

UNGA79: Bayan Najeriya ta ranto N87.38trn, Tinubu ya nemi afuwa ga kasashen Afrika

Fadar shugagan kasa ta yi magana kan yiwa majalisar ministoci garambawul
Shugaba Tinubu zai yiwa majalisar ministocinsa garambawul. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Yaushe Tinubu zai yi garambawul?

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 25 ga Satumba inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Onanuga ya yi magana a taron manema labaran tare da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan shafukan sadarwar zamani, O’tega Ogra.

Kakakin shugaban kasar ya bayyana cewa, babu tabbas ko za a yi sauye sauyen kafin ranar 1 ga Oktoba, amma ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba ne za a yi hakan.

Idan dai ba a manta ba tun a watan Agustan 2023a ne shugaba Tinubu ya nada ministocinsa, kuma an yi ta ce-ce-ku-ce kan yi masu garambawul kan rashin aikin da wasu Ministoci ke yi.

Tinubu ya aika sako ga ministoci

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su wataya: Tinubu ya sanya ranar fara biyan sabon albashin N70000

A cewar jaridar muryar Najeriya (VON), Shugaba Tinubu ya umurci ministocinsa da su tallata ayyukan gwamnatinsa da gaske.

A cewar Onanuga, shugaba Tinubu ya bukaci ministocin da su "fita domin yada nasarorin da gwamnati ta samu".

Ya lura cewa wasu ministocin suna shakkar yin magana a bainar jama’a inda ya kara da cewa:

"‘Yan Najeriya da dama sun yi imanin cewa shugaban ba ya yin komai, yayin da a zahiri gwamnatin tarayyar na aiwatar da ayyukan ci gaba sosai."

Tinubu ya jaddada cewa ya kamata ministocinsa su kara maida hankali wajen isar da wadannan nasarori ga jama'a.

Bola Tinubu ya shiga taron FEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya shiga taron majalisar zartarwar tarayya (FEC) a yayin da ake rade-radin zai kori wasu ministoci.

Tinubu, wanda ya sha alwashin korar duk ministan da ya zama ɗan dumama kujera, ya yi gum da bakinsa game da batun garambawul a majalisar zartaswa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.