Kebbi: Ambaliya Ta Wargaza Ƙauyuka, Dubban Mutane Sun Shiga Garari

Kebbi: Ambaliya Ta Wargaza Ƙauyuka, Dubban Mutane Sun Shiga Garari

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa a Sokoto ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a jihar Kebbi a Arewacin Najeriya
  • Shugaban hukumar NEMA a Sokoto, Aliyu Shehu-Kafindagi ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wajen da aka yi ambaliyar
  • Rahotanni da suka fito sun nuna cewa ambaliyar ta wargaza ƙauyuka da dama, mutane sun rasa gidaje masu yawa da gonakin da suke noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta fitar da rahoto kan ambaliyar ruwa da aka yi a jihar Kebbi.

NEMA ta bayyana cewa ambaliyar ta jawo asara mai dimbin yawa ga al'ummar da ambaliyar ta ritsa da su.

Kara karanta wannan

Kano, Katsina: Jerin jihohi 15 da za a kwashe kwanaki 5 ana zabga ruwa da iska

Ambaliyar ruwa
Ambaliya ta yi barna a jihar Kebbi. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban hukumar NEMA a jihar Sokoto, Aliyu Shehu-Kafindagi ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi ambaliyar ruwa a jihar Kebbi

Hukumar NEMA ta sanar da cewa an samu ambaliyar ruwa a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

Bincike ya nuna cewa ambaliyar ta faru ne sakamakon ruwan sama da aka samu a tsakanin 17 zuwa 22 ga Satumba.

Ambaliya ta wargaza ƙauyuka a Kebbi

Rahotanni da suka fito sun nuna cewa ambaliyar ta yi barna sosai inda ta wargaza kimanin ƙauyuka goma ciki har da Kunda, Dala-Maiwada da Dala-Mairuwa.

Sauran ƙauyukan sun hada da Ishe-Mairuwa, Kwarkusa, Kumurdi, Tugar, Maigani da kuma kauyen Gundu.

Ambaliya: Mutane 2,000 sun rasa gidaje

Premium Times ta wallafa cewa kididdigar hukumar NEMA ta nuna cewa mutane sama da 2,000 ne suka rasa gidaje a kauyukan.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da jajantawa Maiduguri, ambaliya ta sake yin barna a Arewa

Bayan haka, mutanen sun rasa gonakinsu kuma yanzu haka sun shiga garari suna neman matsuguni.

NEMA ta tabbatar da cewa an samar da sansanin yan gudun hijira a wata makaranta inda ta samu mutane 300.

Gwamnati ta yi gargadi kan ambaliya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ambaci wasu jihohin da za su fuskanci barazanar ambaliyar ruwa sosai.

Gwamnatin tarayya ta ambaci lokacin da ambaliyar ruwan za ta yi ƙamari saboda al'ummar Najeriya su shirya dabarun kare kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng