UNGA79: Shugaba Tinubu Ya Koda Najeriya, Ya Ce Afrika ba Ta Bukatar Tallafi daga Kasashe

UNGA79: Shugaba Tinubu Ya Koda Najeriya, Ya Ce Afrika ba Ta Bukatar Tallafi daga Kasashe

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana muhimmancin da nahiyar Afrika ke da shi a wajen ci gaban manyan kasashen duniya
  • Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shetiima yawakilta ne ya bayyana haka yayin taron Majalisar Dinkin Duniya
  • Ya ce a yanzu haka, duniya na bukatar nahiyar saboda tarin albarkatun kasa da yankin ke da shi, ya ce ba su da bukatar tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

New York, US - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya koda irin albarkatun kasa da Najeriya ke da su a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79.

Shugaban, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima yayin taron ya bayyana cewa nahiyar Afrika baki daya na cike da albarkatun kasa da za su inganta tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki: Kungiyar APC na shirin daukaka kara kan nasarar Ganduje

Kashim
Shugaba Tinubu ya fadi muhimmancin Afrika ga duniya Hoto; Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa wannan dalili ya sa bai dace nahiyar ta rika jiran tallafi da taimako daga sauran kasashen duniya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya fadi muhimmancin Afrika

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce yankin Afrika na da tarin albarkatun kasa, wanda duniya ke bukata a halin yanzu.

Ya ce yalwar arzikin da ke dunkule a Afrika ya sa duniya ke bukatar nahiyar fiye da yadda nahiyar ke bukatar sauran kasashen duniya.

Shugaba Tinubu ya koka kan kasuwanci

Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu ya koka kan rashin daidaito wajen kasuwancin tsakanin nahiyar Afrika, Caribbean da Pacific da kuma Kungiyar tarayyar Turai.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da nahiyar za ta fita daga kangin talauci yayin da da ake kokarin samun yancin siyasa da tattalin aziki.

Kara karanta wannan

UNGA79: Bayan Najeriya ta ranto N87.38trn, Tinubu ya nemi afuwa ga kasashen Afrika

Tinubu ya nemi yafiyar basussukan Afrika

A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika kokon barar neman kasashen duniya da sauran hukumomi su yafe basussukan da kasashe masu tasowa na Afrika su ka karba.

Shugaban, ta bakin mataimakinsa, Kashim Shetiima ne ya mika bukatar a taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York, Amurka, inda ya ce hakan zai taimaki nahiyar sosai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.