Zanga Zangar Oktoba: 'Yan Sanda Sun Fadi Dalilin Gayyatar Shugaban Matasa
- Yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024, yan sanda a Lagos sun gayyaci shugaban matasa
- Kwamishinan yan sanda a jihar, Olanrewaju Ishola ya ce sun dauki matakin ne domin tattauna wasu batutuwa kan lamuran kasa
- Yan sanda sun gayyaci shugaban kungiyar 'Take it Back Movement', Juwon Sanyaolu da ya jagoranci zanga-zanga a Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Rundunar yan sanda ta gayyaci shugaban masu shirya zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024.
Rundunar ta gayyaci Juwon Sanyaolu wanda ke jagorantar kungiyar 'Take it Back Movement' da ta yi zanga-zanga a watan Agustan 2024.
Zanga-zanga: Yan sanda sun kira shugaban matasa
Kwamishinan yan sanda, Olanrewaju Ishola shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da The Guardian ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ishola ya ce sun gayyaci Sanyaolu ne da sauran mambobinsa domin tattaunawa kan lamura da dama da suka shafi Najeriya.
Za a gudanar da ganawar a yau Laraba 25 ga watan Satumbar 2024 a ofishin kwamishinan da ke Ikeja a Lagos.
Dalilin neman shugaban masu zanga-zanga
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya bayyana yadda ganawar za ta kasance.
Hundeyin ya ce ganawa ce ta musamman amma babu shirin cafke wani daga cikinsu, cewar rahoton Punch.
"Shirin gudanar da zanga-zangar ranar 1 ga watan Oktoban 2024 na daga cikin abin da za a tattauna."
"Ba fada ba ne ko kuma wani tashin hankali, ko da bai halarta ba, babu wani abu da zai faru."
- Benjamin Hundeyin
Zanga-zanga: Matasa sun lissafo bukatu ga Tinubu
Kun ji cewa matasan Najeriya na cigaba da shirye shiryen gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a karo na biyu.
A wannan karon, matasan sun fitar da wasu jerin bukatu 17 domin Gwamnatin Tarayya ta cika musu domin hana zanga-zanga.
Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zanga-zanga daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 saboda halin rayuwa da aka shiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng