Zargin Almundahana: Kotu Ta Dage Shari'ar Yahaya Bello da Hukumar EFCC
- Babbar kotun tarayya, mai zamanta a Abuja, ta dage sauraron zargin almundahana da ake yi wa tsohon gwamna, Yahaya Bello
- Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ce ke zargin tsohon gwamnan da handame sama da N80bn daga asusun Kogi
- Mai Shari'a Emeka Nwite ya dage sauraron shari'ar zuwa watan Oktoba, inda ake jiran hukuncin kotun koli kan karar da Bello ya shigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraren shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da za a yi a yau zuwa watan gobe.
Mai Shari'a Emeka Nwite ne ya bayyana hukuncin a ranar Laraba bayan tsohon gwamnan ya nufi kotun koli domin neman a soke umarnin kama shi da babbar kotu ta yi.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), na zargin Yahaya Bello da almundahana da halasta kudin haram.
Yahaya Bello ya nufi kotun koli
Jaridar Independent ta wallafa cewa lauyan Yahaya Bello, A.M Adoyi ya shaidawa kotu cewa zaman na yau Laraba ba zai yiwu ba saboda maganar na gaban kotu ta gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barista A.M Adoyi ya kara da cewa abin da ya dace kotu ta yi shi ne dakatar da shari'ar har sai kotun koli ta yanke hukunci kan karar da Yahaya Bello ya shigar.
EFCC ta soki lauyan Yahaya Bello
Lauyan hukumar EFCC, Kemi Pinheiro SAN ya zargi lauyan Yahaya Bello da kokarin mayar da kotu wajen wasa da raha.
Ya kara da cewa ko a baya, kotun daukaka kara ta soke bukatar Yahaya Bello na kalubalantar hanyar da EFCC ke bi na gurfanar da shi gaban kotu.
Mai Shari'a Emeka Nwite ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 Oktoba, 2024.
Yahaya Bello na wasan buya da EFCC
A baya mun ruwaito cewa bayan an samu musayar kalamai tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamna Yahaya Bello, tsohon gwamnan ya tsere inda ake nemansa yanzu ruwa a jallo.
Duk da Yahaya Bello ya bayyana cewa ya mika kansa ga hukumar EFCC, amma hukumar ta musanta batun, inda ta bayyana cewa tsohon gwamnan ya yi batan dabo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng