Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya, An Samu Bayanai

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya, An Samu Bayanai

  • Majalisar dattawan Najeriya ta fara tantance Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alƙalai a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar ta tabbatar da naɗin a wata wasiƙa da ya aika ranar Talata
  • Rahotanni sun bayyana cewa Kudirat Kekere-Ekun ta isa zauren majalisar da misalin karfe 12:00 na rana tare da alkalan kotun koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawa ta fara tantance Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya watau CJN.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta Tsakiya) shi ne ya fara gabatar da batun a matsayin wanda za a karya da shi a zaman yau Laraba.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu, ta tabbatar da naɗin CJN a Najeriya

Majalisar dattawa.
Majalisar dattawa ta fara aikin tantance Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alƙalai CJN Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Muƙaddashin CJN ta dura zauren majalisa

Vanguard ta ce Kudirat Kekere-Ekun da kwamitin da ya ƙunshi ɗaukacin ƴan majalisar dattawa zai tantance, ta isa zauren da misalin karfe 12.30 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta samu izinin shiga majalisar tare da tawagar alkalan kotun ƙoli da na kotun ɗaukaka ƙara bayan Sanata Bamidele ya bukaci jingine doka ta 12 bisa al'ada.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado shi ne ya jagoranci muƙaddashiyar CJN zuwa zauren majalisa domin tantance ta.

Kudirat ta zama CJN ta 23 a Najeriya

Idan ba ku manta ba shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin CJN na 23 a tarihi a watan da aya gabata.

Bayan rantsar da ita, sabuwar shugabar alkalan ta ci gaba da aiki a matsayin rikon kwarya kafin majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da naɗinta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bauchi ta gabatar da kasafin kudi gaban majalisa, ta fadi aikin da za ta yi

A halin yanzu dai majalisar ta fara tantance sabuwar CJN kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, Channels tv ta ruwaito.

Tinubu ya yi fatali da wani kudirin majalisa

A wani rahoton kuma shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da kudirin dokar da ya nemi tsawaita wa’adin shekarun ritaya na ma’aikatan majalisar tarayya

Ƙudirin dokar ya nemi a kara shekarun ritayar ma'aikatan zuwa 65 (na haihuwa) ko kuma shekaru 40 (na gudanar da aikin gwamnati).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262