Dubu Ta Cika: An Kama Barawon da Yake Fasa Kabari domin Sata a Maƙabarta
- Rundunar yan sandan Najeriya ta reshen jihar Bauchi ta cafke wani matashi da ake zargi da fasa kabari yana sace karafuna
- Matashin dan shekaru 21 ya ce idan ya sace karafuna bayan ya fasa kabari yana sayar da su ne ga baban bola domin samun kudi
- Bayan amincewa da aikata laifin, matashin ya bukaci idan aka mika shi gaban alkali domin shari'a a masa gafara saboda ya tuba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda ta cafke wani matashi dan shekaru 21 da zargin zuwa maƙabarta domin aikata sata.
Ana zargin matashin ne da aikata laifin fasa kabari da aka birne mutane, yana zuwa ya fasa kabari domin cire karafuna.
Legit ta gano yadda lamarin ya faru ne a wani bidiyo da rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama matashi mai fasa kabari
Rundunar yan sandan Najeriya ta sanar cafke wani matashi a jihar Bauchi da ake zargi da sata a kabari.
Matashin ya amsa cewa yana rusa kabari ne domin ya cire karafuna da aka yi ginin kabarin domin samun kudin kashewa.
Yadda aka kama ɓarawo mai fasa kabari
Mutumin da ake zargin ya bayyana cewa yan kwamitin unguwa ne suka kama shi yayin da suka ga ya dauko karafuna.
Bayan kama shi sai suka mika shi ga rundunar yan sanda domin su yi bincike da tabbatar da gaskiyar lamarin.
A ina ɓarawon ke kashe kudin karafuna?
Wanda ake zargin ya bayyana cewa idan ya fasa kabari ya saci karafuna yana sayarwa baban bola ne.
Yayin da yake bayani, ya bayyana cewa yana sayen kayan shaye-shaye ne kamar su tabar wiwi da tabar sigari idan ya sayar da karafunan.
Sai dai ya bukaci a yi masa afuwa saboda cewa wannan ne karon farko da ya aikata laifin kuma ya tuba.
An kama yan fashi a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani gungun yan fashi da suka addabi mutane a karamar hukumar Misau.
Ana zargin cewa yan fashin sun shiga wani gida da bindiga suka kwace makudan kudi da kayayyaki masu muhimmanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng