‘Matsalolin Sun Yi Yawa,’ Za a yi Taro domin Tunkarar Tinubu da Murya 1

‘Matsalolin Sun Yi Yawa,’ Za a yi Taro domin Tunkarar Tinubu da Murya 1

  • Kwamitin zaman lafiya a Najeriya zai yi wani zama domin duba yadda za a magance matsalolin da suka addabi al'ummar Najeriya
  • Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ne zai jagoranci zaman a birnin tarayya Abuja domin duba yadda za samu sauki a Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa an gayyaci kungiyoyi da masana domin tattaunawa kan yadda za a magance tarin matsalolin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kwamitin zaman lafiya na Najeriya (NPC) ya shirya wani taro domin duba hanyar da za a saukaka lamura a Najeriya.

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar da Rabaran Matthew Hassan Kukah ne za su jagoranci zaman.

Kara karanta wannan

Zanga zangar Oktoba: Matasa sun fitar da zafafan bukatu 17 ga Tinubu

Bola Tinubu
Kwamitin zaman lafiya zai yi taro kan matsalolin Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kwamitin ya gayyaci masana da kungiyoyi domin tattaunawa yayin taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake fatan samun sauki a Najeriya

Kwamitin zaman lafiyar ya fitar da sanarwar cewa yan Najeriya sun saka tsammanin samun saukin rayuwa bayan zaben 2023.

A karkashin haka ne ma kwamitin ya ce aka samu yan Najeriya da dama suka fito zaben domin neman sauyi.

Yan Najeriya na shan wahala inji NPC

Sai dai kwamitin zaman lafiyar ya ce fatan samun sauƙin bai samu ba bayan zaben saboda tsare-tsaren gwamnati.

Sahara Reporters ta wallafa cewa NPC ya ce wahalar rayuwa na cikin abubuwan da suka sanya yan Najeriya fitowa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Agusta.

Za a yi taron neman mafita a Najeriya

A ranar 26 ga Satumba ne kwamitin zai zauna a Abuja domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalolin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Sama da mutum miliyan 88 na fama da talauci," Sheikh Pantami ya ba matasa mafita

Rahotanni sun nuna cewa za a tattauna ne tsakanin masana da kungiyoyi domin tunkarar gwamnati da murya daya kan matsalolin Najeriya.

Tinubu ya rarrashi yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kara yin kira na musamman ga yan Najeriya kan halin wahalar rayuwa da ake ciki a kasar nan.

An ruwato cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin cewa nan gaba kadan yan Najeriya za su murmure a kan halin da suke ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng