“Ni ba Malalaciya ba ce”: Zainab Bayero Ta Sake Magana kan Halin da Suke ciki
- Yar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ta koka kan yadda mutane suka dira kansu saboda neman taimako da suka yi
- Zainab Bayero ta ce dan Adam yana neman taimako ne musamman idan wadanda suke da hakkin kulawa da shi suka guje shi
- Diyar marigayin ta bayyana yadda aka rika kwatanta da malalaciya saboda ta nemi taimako inda ta ce sam ba haka ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Diyar marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero ta sake yin magana kan kalubalen da suke fuskanta.
Zainab Ado Bayero ta ce mutane da dama sun yi ta sukarta kan maganganun da ta yi a bayan kan halin da suke ciki.
Zainab Bayero ta koka kan halin mutane
Diyar marigayin ta bayyana haka ne yayin hira da jaridar Tribune a yau Laraba 25 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zainab ta ce mutane sun yi ta kiranta malalaciya saboda neman taimako inda ta ce hakan ba daidai ba ne.
Ta ce daukar matakin neman taimako ba lalaci ba ne illa neman hanyar tsira daga halin da suke ciki.
"Ni ba malalaciya ba ce" - Zainab Ado Bayero
"Mutane sun kwatanta ni da malalaciya ko kuma meyasa na ke roko, ba ina roko ba ne saboda ni malalaciya ba ce, ina yi ne saboda rayuwa."
"Misali, Dan sarki Harry ya je Amurka inda Tyler Perry ya ba shi gida, ba wai domin ya roka ba sai dai neman taimako, haka dan Adam ya ke."
"Mahaifiyata ta taimakawa mutane a baya maza da mata amma yanzu mun shiga wannan yanayi kuma an yi mana wata irin fahimta."
"Ana magana wai meyasa muke neman taimako bayan daga gidan sarauta muke? Ana bukatar taimako wani lokaci musamman idan wadanda ya kamata su baka kulawa da so sun guje ka":
- Zainab Ado Bayero
Mahaifiyar Zainab Bayero ta roki Tinubu
Kun ji cewa yayin da ake sukar Zainab Ado Bayero, mahaifiyarta ta yi magana kan halin da suke ciki da gwagwarmayar da suka yi a baya.
Hauwa Momoh wacce yar marigayi Otaru na Auchi ce ta ce tun bayan mutuwar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero suka fada matsala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng