UNGA79: Bayan Najeriya ta Ranto N87.38trn, Tinubu Ya Nemi Afuwa ga Kasashen Afrika
- Bola Ahmed Tinubu ya roki kasashe masu karfin tattalin arziki da hukumomin duniya su yafewa Afrika rancen da aka karbo
- Shugaban ya nemi yafiyar ta bakin mataimakinsa, Kashim Shettima a taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York
- Ya ce yan Najeriya da sauran kasashen da za a yafewa dimbin basussukan za su mori tsarin sosai idan hakan ta samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
New York, US - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kwaiwayi sakon tsofaffin shugannin kasar nan wajen mika bukatar yafe wa Najeriya da kasashe masu taso wa basussukan da su ka ci.
Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS ya bayyana bukatar a taron majalisar dinkin duniya na 79 da ke gudana a New York, Amurka.
Channels Television ta wallafa cewa shugaban kasar nan ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda ya shaida wa taron kasashen dalilin neman afuwa kan basussukan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu: Dalilin neman yafiyar basussuka
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Tinubu na ganin yafe wa kasashe masu tasowa dimbin bashin da su ka ci zai ba su damar gudanar da ayyukan ci gaban al'umarsu.
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da babban mataimaki na musamman a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya fitar a ranar Talata.
"UN ba za ta kula Tinubu ba," Masani
Masanin tattalin arzikin kasar nan, Dr. AbdulNaseer Kurawa Yola na jami'ar tarayya da ke Dutse, ya shaida wa Legit cewa zai yi wahala kasashen waje su dauki bukatar kasar nan da muhimmanci.
Ya ce a lokacin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, sai da aka tabbata babu kasar da ke bin Najeriya bashi.
Dr. AbdulNaseer na ganin irin rayuwar da shugabannin kasar nan ke yi, kamar sayen jirgin sama na alatu ga shugaba ya nuna cewa ba da gaske ake son gyara tattalin arzikin kasa ba.
Bashin Najeriya ya karu da N24trn
A baya mun ruwaito cewa ofishin kula da basussuka na kasa (DMO) shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kara ciyo bashin Naira tiriliyan 6.53 tsakanin watan Disambar 2023 zuwa Maris 2024.
Wannan na nufin bashin da ake bin kasar nan ya karu da akalla Naira tiriliyan 121.67 a cikin watanni uku kawai, inda aka karbo rancen kudin daga ciki na wajen Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng