Yan Sanda Sun Kwana ciki, Sun Bar Abin N800,000 a Inda Suka Yi 'Zaluncin' N1,000

Yan Sanda Sun Kwana ciki, Sun Bar Abin N800,000 a Inda Suka Yi 'Zaluncin' N1,000

  • Bayan abin da ake zargin ya faru da Seaman Abbas Haruna, an sake bankaɗo labarin zaluncin da ƴan sanda suka yi wa wani mutumi a gidan mai
  • Mai gabatar da shirin Brekete Family ne ya bayar da labarin, ya ce ƴan sandan da suka aikata laifin sun bar kayan aikinsu mai darajar N800,000
  • Ya ce jami'an sun karɓi N1,000 daga nutumin bayan sun gama bincikensu ba su kama shi da laifin komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayan fallasar irin azabtarwar da aka yi wa Seaman Abba Haruna a gidan sojan Najeriya, wani labarin zaluncin ƴan sanda ya sake bayyana kwanan nan.

Ana zargin ƴan sandan waɗanda a yanzu ba a tantance ko su waye ba sun zalunci wani bawan Allah wanda ke fama da rayuwa, sai dai sun bar abu mai muhimmanci.

Kara karanta wannan

"Sama da mutum miliyan 88 na fama da talauci," Sheikh Pantami ya ba matasa mafita

Sufetan yan sandan Najeriya.
Yadda wasu yan sanda suka bar kayan aikin N800 000 bayan zaluntar wani bawan Allah Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ahmed Isah, mai gabatar da shirin Brekete Family, gidan radiyo da talabijin na Human Right, shi ne ya ba da labarin mutumin, amma bai faɗi sunansa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya ƙi yarda mutumin da aka zalunta ya halarci shirin ne saboda ka da wani abu mara daɗi ya biyo baya idan ƴan sandan suka gane shi.

Yadda ƴan sanda suka cuci mutumin

A labarin da ya bayar, Ahmed Isah ya ce mutumin ya shiga gidan mai domin sayen fetur a mota, ba zato ƴan sanda suka kama shi.

"Wani mutum da ke fama da rayuwa, ba zan nuna maku shi saboda ka da su kama shi, ya je sayen mai, ƴan sanda suka kama shi, suka nemi takardu ya ba su, suka bincike motar har da fitila duk da safiya ce, komai dai tsaf."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige limamin masallaci har lahira a Abuja, sun sace mutum 1

"Ƴan sandan nan dai suka duba suka duba, sai suka ce ai tayar motarsa ɗaya ba ta da kyau, mutumin ba shi da ko sisi, hatta man da ya saya rancen kuɗin ya yi, suka ce sai ya ba su kuɗi.
"Tun daga manyan kuɗi har aka dawo N2,000, mutumin nan ya ce ba shi da su, haka suka yi tirka-tirka har aka dawo N1,000, haka mutumin ya je ya ranto kuɗin ya ba su."

- In ji Ahmed Isah.

Ƴan sanda sun mance da oba-oba

Mai gabatar da shirin ya ce abin mamakin da ban dariya shi ne ƴan sandan sun manta da oba-obarsu ta aiki da ta kai darajar N800,000.

A faifan bidiyon, Ahmed ya nuna wa mahalarta shirin oba-obar da ƴan sandan suka bari, kana ya buƙaci kwamishinan rundunar ƴan sandan Abuja ya bincika.

Ya ce sai ƴan sandan nan sun maido wa bawan Allah kuɗinsa sannan za a ba su wannan oba-oba.

Kara karanta wannan

Wata tanka maƙare da man fetur ta fashe, ta yi wa mutane illa a birnin Abuja

Rundunar ƴan sanda ta yi rashi

A wani rahoton kuma kun ji cewa wasu jami'an rundunar 'yan sandan Kano sun rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a titin Zaria-Kano.

An ruwaito cewa hatsarin mota ya rutsa da kimanin jami'an 'yan sandan 15 a hanyarsu ta komawa Kano daga aikin zaben da suka yi a Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262