"Yan Kasuwa ba za Su Iya Sayo Fetur daga Matatar Dangote ba:" PENGASSAN
- Kungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas ta kasa ta ce za a iya samun matsala kan farashin man fetur a Najeriya
- Wannan kungiyar na ganin yan kasuwa za su sayar da kowace litar fetur a kan sama da N1000 nan gaba a gidajen mai
- Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya ce matsala za ta samu idan yan kasuwa na sayo fetur kai tsaye daga Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas ta kasa (PENGASSAN), ta ce za a samu matsala idan yan kasuwa su ka fara sayo fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Kungiyar dillalan fetur (IPMAN) ta sha nanata cewa za a samu saukin farashin fetur idan kamfanin NNPCL ya sahale ma ta sayo fetur kai tsaye daga Dangote.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar PENGASSAN na ganin sayen fetur kai tsaye daga matatar ba zai zo wa da yan kasa sauki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"NNPCL na sayo fetur da tsada:" PENGASSAN
Kungiyar PENGASSAN ta bayyana cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) na sayo fetur da tsada, sannan ya sayar wa yan kasuwa da sauki saboda a saukaka wa yan kasa.
Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya shaida wa manema labarai cewa NNPCL kan sayi kowace lita a kan N950 daga Dangote, a sayar wa yan kasuwa kan N700.
"Za a fuskanci tsadar fetur:" PENGASSAN
Shugaban kungiyar PENGASSAN, Festus Osifo ya ce idan yan kasuwa za su sayi fetur kai tsaye daga matatar Dangote, za su saya kan farashin da NNPCL ke sayo wa.
Saboda haka dole ne yan kasuwar su sayar kan sama da N1,000, shiyasa yan kasuwa masu zaman kansu su ka fi son saya daga NNPCL.
PENGASSAN ta fadi dalilin karancin fetur
A wani labarin kun ji cewa kungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas ta ce tsarin da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ke bi wajen rarraba fetur babbar matsala ce.
Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya ce tsarin da ake amfani da shi ya tsufa, saboda haka dole a sabunta hanyar rarraba fetur ga gidajen mai domin ya wadata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng