Rashin Tsaro: Janar Taoreed Lagbaja Ya Bayyana Matsalar da Sojoji Ke Fuskanta

Rashin Tsaro: Janar Taoreed Lagbaja Ya Bayyana Matsalar da Sojoji Ke Fuskanta

  • Babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Taoreed Lagbaja, ya koka kan ƙarancin jami'an tsaron da ake da su
  • Taoreed Lagbaja ya bayyana cewa jami'an tsaron da ake da su ba za su iya kare ƴan Najeriya mutum miliyan 200 ba
  • Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda rundunar sojojin Najeriya ke dogaro da kayan da aka shigo da su daga ketare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Taoreed Lagbaja, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

Taoreed Lagbaja ya bayyana cewa jami’an tsaro miliyan biyu da ake da su a ƙasar nan ba za su iya kare al’ummar Najeriya sama da miliyan 200 ba.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin 'yan bindiga: Gwamna Dauda ya dauki mataki kan Matawalle

Lagbaja ya koka kan karancin jami'an tsaro
Lagbaja ya ce jami'an tsaro ba za su iya kare 'yan Najeriya ba Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Shugaban sojojin ƙasan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Lagbaja ya ce kan rashin tsaro?

Lagbaja ya koka kan yadda sojoji ke dogaro da kayan aiki da ake shigowa da su daga ƙasashen waje saboda raunin masana'antun ƙasar nan, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Hafsan sojojin ya kuma nuna damuwarsa kan rashin isassun kuɗi ga rundunar sojojin Najeriya (AFN), wanda ya ce hakan yana matuƙar shafar ayyukan sojojin.

"A ƙasar da ke da mutane sama da miliyan 200, ba daidai ba ne a yi tsammanin jami'an tsaro, kusan miliyan biyu, ciki har da sojoji sama da 100,000 za su iya kare ɗaukacin al'ummar ƙasar."
"A shekarar 2023, rundunar sojojin Najeriya na da kasafin kusan $2.8bn, tare da ƙarin kasafin kuɗi na kusan $1bn. Sai dai, ba duka kuɗin aka saki ba."

Kara karanta wannan

"Sama da mutum miliyan 88 na fama da talauci," Sheikh Pantami ya ba matasa mafita

"Duk da cewa kuɗin da ake ba wa AFN na ƙaruwa a duk shekara tun daga shekarar 2017, koma bayan tattalin arzikin ƙasar nan ya ruguza ainihin darajar kuɗin da aka ware."
"Rashin kuɗin yana shafar kayan aikin rundunar sojojin Najeriya, wanda hakan yana yin tasiri kan ayyukan da take gudanarwa."

- Taoreed Lagbaja

Lagbaja ya magantu kan juyin mulki

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce sojoji ba za su faɗa tarkon masu kiraye-kirayen juyin mulki ba.

Lagbaja ya bayyana cewa rundunar sojoji ba za ta tsorata ko ta faɗa tarkon manyan masu faɗa a ji da ke kirayen-kirayen sojoji su karɓe iko da ƙasar nan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng