Bola Tinubu Ya Aika Saƙo ga Majalisar Dattawa kan Sabuwar Shugabar Alƙalan Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ya aika saƙo ga majalisar dattawa yana neman ta amince da naɗin Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalai (CJN)
- A watan jiya ne shugaban ƙasar ya naɗa ta a matsayin CJN ta riko bayan bayan Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar Shugaba Tinubu a zauren majalisar ranar Talata, 24 ga watan Satumba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya (CJN).
Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da Tinubu ya aika kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zaman yau Talata, 24 ga watan Oktoba, 2024.
A wasiƙar, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisar cewa sashi na 231(1) a kundin tsarin mulki ya ba shi damar nada CJN bisa shawarin majalisar shari'a (NJC), rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya bukaci majalisa ta amince da naɗin NJC
Shugaban kasar ya bayyana cewa ya gamsu da nadinta bayan shawarin NJC, sannan ya bukaci majalisar dattawa da ta gaggauta tabbatar da hakan.
A ruwayar The Nation, Bola Tinubu ya ce:
"Ina gabatar maku da Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, CON domin tabbatar da naɗinta a matsayin shugabar alkalan Najeriya. Ina da yaƙinin majalisar dattawa za ta amince da wannan buƙata."
Takaitacccen bayani kan sabuwar CJN
Mai shari'a Kudirat mai shekaru 66 a duniya ta zama mukaddashin CJN bayan Mai Shari’a Ariwoola ya yi ritaya a watan da ya shige.
Kudirat Kekere-Ekun ita ce shugabar alkalai na 23 a Najeriya kuma mace ta biyu a fannin shari’a da ta taba kai wa wannan matsayi.
An haife ta ranar 7 ga Mayu, 1958, a birnin Landan na kasar Ingila kuma ta fara karatun shari'a ne a Jami'ar Legas inda ta samu digiri na farko a fannin shari'a a 1980.
Bayan ta kammala karatu, Kudirat Kidirat Kekere-Ekun ta zama cikakkiyar lauya a 1981.
Tinubu na sane da wahalar da ake sha
A wani rahoton na daban Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya sani ana cikin wani hali a Najeriya inda ya zargi gwamnatocin baya.
Shugaban ƙasar ya ce dukkan wannan hali da aka shiga na da nasaba da matakan da aka dauka a baya a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng